Trends

Za a Fara Samun Fasfo a Cikin Kwana 7 – Gwamnatin Tarayya

Olubunmi Tunji-Ojo Ministan cikin gida

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa nan ba da jimawa ba za su rika samun fasfo dinsu cikin kwanaki bakwai kacal bayan kammala aikace-aikace.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana haka, inda ya ce hakan zai yiwu ne sakamakon inganta kayan aikin Hukumar Shige da Fice ta Kasa (NIS).

Da yake magana bayan duba sabuwar cibiyar Data Personalisation da aka kammala a Hedikwatar Hukumar da ke Abuja a ranar Alhamis, Ministan ya bayyana wannan mataki a matsayin “mai sauya fasalin” tsarin samar da fasfo a Najeriya.

Ya ce cibiyar za ta rage lokacin jiran aiki, domin yanzu ana iya buga fasfo cikin awa 24 sannan a isar da shi cikin mako guda.

Ministan ya bayyana cewa tsoffin injinan da ake amfani da su na iya sarrafa fasfo 250 zuwa 300 kacal a kowace rana, amma sabuwar fasaha yanzu tana iya samar da fasfo kusan 1,000 a kowane awa, abin da ke baiwa NIS damar samar da fasfo 4,500 zuwa 5,000 a rana.

“Wannan yana nufin cewa duk wanda aka amince da aikace-aikacensa zai iya tsammanin fasfonsa ya fito cikin awa 24,” in ji shi.

Tunji-Ojo ya ƙara da cewa wannan shi ne karon farko tun kafa Hukumar Shige da Fice a 1963 da Najeriya za ta fara aiki da cibiyar da ta kai matsayin duniya wajen sarrafa fasfo, wacce za a iya kwatanta da irin na Amurka, Birtaniya, Faransa, Rasha, Indiya da Bangladesh.

A cewarsa, sabon tsarin ya kawo ƙarshen tsohon tsarin da ake sarrafa fasfo a cibiyoyi 96 a Najeriya da ƙasashen waje — tsarin da ya bayyana a matsayin “mai rauni kuma mara inganci.”

Ministan ya kuma tuna cewa gwamnati ta gada sama da aikace-aikacen fasfo 200,000 da suka taru a baya, amma ya jaddada cewa sabon tsarin ya kawar da irin waɗannan matsaloli ta hanyar sarrafa bayanai ta atomatik da rage tsoma bakin ɗan adam.

“Wannan aikin yana tabbatar da cewa zamanin jinkirin aiki ya ƙare. Jami’ai ba za su ƙara yin aiki dare da rana domin share tarin aikace-aikace ba. Yanzu tsarin ya zama kai tsaye, cikin sauri kuma mai sauƙin bin diddigi,” in ji shi.