Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ya yi magana da Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, a ranar Laraba kafin shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar da kawo karshen dokar ta-ɓaci a jihar.
Wike ya ce bayan watanni shida na dokar ta-ɓaci a jihar mai arzikin man fetur ta Kudu maso Kudu, an samu zaman lafiya, kuma dukkan masu ruwa da tsaki sun amince da ci gaban jihar.
“Yanzu ina gaya muku, jiya na yi magana da gwamna (Fubara). Na shaida masa cewa zan tafi daren nan in dawo, shi kuma ya ce zai tafi da safiyar yau,” in ji Wike a tattaunawa da Politics Today na Channels TV a ranar Alhamis.
“Don haka, zan iya cewa da ikon Allah zaman lafiya ya dawo. Kuma ku dubi abin da Majalisar Dokoki ta yi yau don saita hanya — za ku ga zaman lafiya; za ku ga shiri ne na ci gaban jihar. Mu ci gaba gaba ɗaya.”
Da aka tambaye shi wa ya fara kiran ɗayan, Wike ya ce ba muhimmanci bane a sani, abin da ya fi muhimmanci shi ne zaman lafiya ya dawo a jihar.
Tun a watan Maris ne Shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da kuma Majalisar Dokoki ta jihar, bayan rikicin siyasa mai tsawo tsakanin gwamnan da Wike.
Wike ya ƙara da cewa ya riga ya yafewa Fubara, kuma babu wani rikici tsakaninsa da wanda ya gaje shi a mulki.
Ya ce, “Na riga na bayyana cewa muna magana da juna. Ba zan yi magana da mutum da ban yafewa ba. Komai ya ƙare. Ba ni ɗan siyasar da zai faɗi abu yau, gobe ya musanta shi. Dole mu ci gaba gaba ɗaya.”
Ministan FCT ya kuma zargi wasu da cewa ba sa son a samu zaman lafiya a jihar, inda ya ce ba sa kawo mafita, sai dai ƙara hura wutar rikici.
“Abin takaici, akwai mutanen da ba sa son zaman lafiya. Yau na kalli wasu suna karkatar da doka, suna cewa akwai rashin doka a zaɓen kananan hukumomi.
“Amma ku tambaye su: me suka yi tun farko don hana wannan rashin doka? Idan kuka ji su suna ihu da surutu, za ku yi tunanin suna da mafita — amma babu abin da suke yi sai ƙoƙarin tayar da rikici. Shugaban kasa ya yi mana abin alheri sosai, kuma zaman lafiya ya dawo.”



