Sowore ya Maka DSS, Meta da X a kotu kan Tauye Haƙƙin Faɗar Albarkacin Baki

Dan gwagwarmaya Omoyele Sowore

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC) a zaɓen 2023, Omoyele Sowore, ya shigar da ƙarar haƙƙin ɗan Adam guda biyu a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan Hukumar Tsaro ta Ƙasa (DSS), da manyan kamfanonin kafafen sada zumunta – Meta (Facebook) da X Corp.

Wata sanarwa da tawagar lauyoyinsa suka fitar a ranar Talata mai ɗauke da sa hannun Tope Temokun ta bayyana cewa an shigar da ƙarar ne domin kalubalantar abin da suka kira “hana magana ba bisa doka ba” da aka yi wa asusun Sowore na Meta da X.

Temokun ya bayyana cewa wannan ƙara ta shafi “tsira da ci gaban ‘yancin magana a Najeriya,” yana mai ƙara da cewa: “Idan hukumomin gwamnati za su riƙa umartar manyan kafafen sada zumunta su fayyace wa wa zai yi magana da abin da za a faɗa, to babu ɗan Najeriya da zai tsira. A kowane lokaci za a iya kashe murya idan masu mulki suka ga dama.”

Ya ci gaba da cewa: “Hana sukar gwamnati ba ya cikin dimokuraɗiyya. Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, sashe na 39, ya bai wa kowane ɗan ƙasa ‘yancin faɗar albarkacin baki ba tare da tsangwama ba. Babu wata hukuma, komai ƙarfinta, da za ta iya soke waɗannan haƙƙoƙi.”

Lauyoyin Sowore sun kuma gargadi Meta da X cewa idan suka lamunci bukatun da ba bisa doka ba na hana magana, hakan yana nufin sun shiga cikin aikata danniya.

Sun ce: “Ba za su iya fakewa da cewa suna tsakiyar magana ba, a daidai lokacin da ake mayar da kafafensu kayan aikin mulkin danniya.”

Tawagar lauyoyin ta nemi kotu ta tabbatar da abubuwa uku:

  1. DSS ba ta da ikon hana ‘yan Najeriya magana a shafukan sada zumunta.
  2. Meta da X ba su da hurumin bayar da kafafensu don a yi amfani da su wajen danniya.
  3. A tabbatar da haƙƙin Sowore da sauran ‘yan Najeriya gaba ɗaya daga kowace irin hana magana da ba bisa doka ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa: “Muna kira ga masu kishin ‘yanci, ‘yan jarida, masu kare haƙƙin ɗan Adam, da al’ummar Najeriya gaba ɗaya su tsaya tsayin daka. Yau @YeleSowore aka fara, gobe wataƙila kai ne. Wannan ba batun mutum ɗaya ba ne – batun ƙa’ida ne. Kuma ba za mu bari Najeriya ta zama ‘dijital ɗiktatanci’ ba.”

Shigar da wannan ƙara ta zo ne sa’o’i kaɗan bayan DSS ta shigar da ƙarar tuhuma mai ɗauke da maki biyar a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, kan Sowore, inda ta kuma haɗa X Corp da Meta Inc. (Facebook) a matsayin waɗanda ake ƙara.

Daraktan Sashen Gurfanarwa na Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya, Muhammed Abubakar, tare da wasu lauyoyin DSS ne suka shigar da ƙarar a madadin hukumar da gwamnatin tarayya.

A ranar 8 ga watan Satumba, DSS ta bai wa Sowore wa’adin sati guda da ya goge wani rubutu a shafinsa da suka ce “ƙarya ce, mai ɓatanci kuma mai tada hankali” kan shugaban ƙasa Bola Tinubu.

Wa’adin ya ƙare a ranar Litinin ba tare da Sowore ya goge rubutun ba. Duk da haka, kamfanonin X da Meta (Facebook) suma sun ƙi amincewa da buƙatar DSS ta rufe asusun Sowore.