Kotun Shari’a ta No. 1 da ke Kofar Kudu a Karamar Hukumar Birnin Kano ta yanke wa ’yan uwa uku hukuncin dauri bisa zargin yin barazana ga mahaifinsu da kuma dukan matarsa, wato mahaifiyarsu ta biyu.
Wadanda aka yanke wa hukuncin sun hada da Sadiq Lawan, Abdussalam Lawan, da Musa Lawan. An gurfanar da su ne a gaban kotu bayan da ’yan sanda suka kama su, inda lauyan gwamnati, Barr. Aliya Aminu Yargaya, ya tuhume su da laifukan hada baki, shiga da karfi, yin barazana, da kuma satar kaya.
Alkalin kotun, Khadi Shamsuddeen Ado Abdullahi Unguwar Gini, ya yanke musu hukuncin wata hudu a gidan yari ko kuma biyan tarar naira 20,000 a kowane laifi, tare da bulalar bulala 20.
Haka kuma, kotun ta kara musu wata hudu dauri ko tarar naira 20,000 a wani laifi daban, tare da karin bulala 20.
Baya ga haka, an umarce su da shafe tsawon watanni shida suna karatun tarbiyya a makarantar Islamiyya domin gyara halayensu.
A matsayin karin hukunci, kotun ta umurce su da su kasance suna wanke wa mahaifinsu kaya na tsawon watanni shida.



