Kungiyan Sharing Hope Za ta Gudanar da Ayyukan Lafiya kyauta a Jos

Kungiyar Sharing Hope wadda za ta yi ayyukan lafiya kyauta a Jos

Kungiyar Sharing Hope Medical Mission USA tare da Sharing Hope Care and Foundation sun sanar da shirin gudanar da kyautattun ayyukan lafiya na makonni biyu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), Jihar Filato, a watan Oktoba 2025.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Mrs. Bridget Omini, shugabar sashen bayani, al’adu da hulɗar jama’a (IPPR) ta JUTH, ta sanya hannu.

A cewar sanarwar, shirin ya biyo bayan gayyatar da Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda Goshwe, ya yi.

An tsara gudanar da aikin lafiya ne a ranar 9 da 10 ga Oktoba, 2025, inda ƙungiyoyin za su kawo likitoci da nas-nas 25 daga gida da ƙasashen waje, waɗanda za su gudanar da muhimman ayyuka kamar:

Bincike da shawarwari na lafiya gaba ɗaya

Manyan da ƙananan ayyukan tiyata

Tiyatar mata (gynecological)

Tiyatar ido

Tiyatar ƙashi (orthopedic)

Kula da hakora

Kula da yara (paediatric care)

Raba magunguna da kayan lafiya kyauta

A cikin sanarwar, ƙungiyar Sharing Hope ta bayyana:

“Mun yi farin cikin amsa kiran Farfesa Goshwe don kawo aikin jinya a Jos. Mun daɗe muna sadaukar da kai wajen dawo da mutunci, rage wahala, da kawo bege ga al’ummomin da ake takura musu a Najeriya sama da shekaru goma.”

Sanarwar ta ƙara da cewa goyon bayan Farfesa Goshwe wajen samar da kayan aiki da tsare-tsare zai taimaka wajen ganin shirin ya yi nasara. Dukkan ayyukan za a yi su kyauta ga jama’a.

One thought on “Kungiyan Sharing Hope Za ta Gudanar da Ayyukan Lafiya kyauta a Jos

Comments are closed.