Trends

Ba El-Rufai ne Jagorana a Siyasa ba – Inji Gwamnan Kaduna, Uba Sani

Gwamna Uba Sani tare da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya musanta jita-jitar cewa yana ƙarƙashin jagorancin siyasa na tsohon gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufai, inda ya jaddada cewa manyan shugabannin da suka haskaka rayuwarsa su ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu da marigayi lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam, Cif Gani Fawehinmi.

Da yake magana a cikin shirin ‘Politics on Sunday’ na TVC, Gwamna Sani ya bayyana cewa ba dole ba ne ya mayar da martani kan maganganun da ke cewa almajirin siyasa ne ga El-Rufai, yana mai cewa hankalinsa ya fi mayar da hankali ne wajen samar da nagartaccen mulki a jihar Kaduna.

“Ban ga dalilin da zai sa in mayar da martani ba,” in ji shi. “Abin da zan iya cewa shi ne akwai mutane da dama da suka taka rawar gani a rayuwata. Tun ma a 1994 na haɗu da Shugaba Bola Tinubu a gidan marigayi Beko Ransome-Kuti. Gani Fawehinmi mahaifi ne a gare ni, domin a lokacin gwagwarmaya na rayu a gidansa. Hankalina ya fi kan Kaduna, ba na magana kan mutane; ba na bari a karkatar da ni, idona yana kan burin da ya dace.”

Gwamnan ya kuma karyata zargin da ake yi cewa gwamnatinsa tana biyan kuɗin fansa ga ‘yan bindiga a yankunan da ke fama da matsalar tsaro, yana mai cewa wannan zargi ƙarya ce da ‘yan siyasa ke yaɗawa domin neman galaba.

“Wasu ‘yan siyasa na wasa da batun tsaro. Jama’a su yi watsi da su. Ba mu taɓa biyan kuɗin fansa ga wani ‘yan bindiga ba,” in ji shi. “Shugabannin al’umma ne suka fito da shawarar hanyar tattaunawa (non-kinetic), na saurare su. Ba mu biya ko kobo ɗaya ba. Duk wanda ya ce akasin haka, yana son yaudarar jama’a ne kawai.”

Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta rungumi dabarun haɗa duka na tsaro da tattaunawa, tana aiki tare da shugabannin al’umma da jami’an tsaro don magance matsalolin tsaro, musamman a Birnin Gwari, inda ya ce matakan al’umma sun fara kawo sakamako.