Ba El-Rufai ne Jagorana a Siyasa ba – Inji Gwamnan Kaduna, Uba Sani
Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya musanta jita-jitar cewa yana ƙarƙashin jagorancin siyasa na tsohon gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufai, inda ya jaddada cewa manyan shugabannin da suka haskaka rayuwarsa su ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu da marigayi lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam, Cif Gani Fawehinmi. Da yake magana a cikin shirin ‘Politics…
