Zaben 2027: Sanata Kabiru Marafa Yayi Alwashin Rage Kuri’un Tinubu

Senata Kabiru Garba Marafa

Tsohon Ɗan Majalisar Dattawan Najeriya mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya, Sanata Kabiru Marafa ya sha alwashin rage wa Tinubu ƙuri’u masu yawa a zaɓen 2027.

Marafa, wanda a baya-bayan nan ya sanar wa BBC ficewarsa daga jam’iyyar APC, bayan ya zargi Tinubu da ”watsar da shi bayan cin zaɓe” ya ce sai ya kawo wa shugaban ƙasar cikas a zɓen 2027 da ke tafe.

Yayin wata hira da hgidan talbijin na Channels, Sanata Marafa ya ce sai ya janyo wa Tinubu asarar kimamin ƙuria’ miliyan guda.

Tsohon ɗan majalisar – wanda ya kasance babban daraktan yaƙin neman zaɓen Tinubu a Zamfara a 2027 – ya ce zai nuna wa shugaban ƙasar matsayinsa a siyasar jihar Zamfara.