Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya jagoranci haɗa kan tsoffin ‘ya’yan jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC) da ke cikin jam’iyyar APC domin mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaben 2027.
Abbas, wanda aka fara zaɓar sa a Majalisar Wakilai a shekarar 2011 a ƙarƙashin tutar CPC, ya bayyana cewa gungun na nan a haɗe kuma sun kuduri aniyar ganin shugaban ya sake samun nasarar tazarce, inda ya jaddada cewa goyon bayansu “ba shi da sharadi.”
Wata sanarwa daga mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Abdullahi Musa Krishi, ta ce Kakakin ya bayyana haka ne a wani taro da Shugaba Tinubu da tsoffin jagororin CPC a Fadar Shugaban Ƙasa ranar Talata. A wajen taron, ya bayyana cewa ƙungiyar ba kawai za ta tsaya a gefen shugaban ba, har ma za ta ƙaddamar da yaƙin neman zabe a fadin ƙasa domin samun goyon bayan tazarcensa.
A cewarsa:
“Yau ce rana ta farko da tsoffin mambobin CPC suka taru cikin irin wannan babbar dama domin nuna goyon baya da godiya ga shugabanmu. A madadin dukkanin mambobin CPC, ina tabbatar maka da goyon bayanmu marar sharadi. Sama da kashi 90% na waɗanda suka taka rawar gani a CPC suna nan a wakilta.”
Abbas ya bayyana cewa za a kafa ƙungiyar “Tsoffin Mambobin CPC don Asiwaju” a matakan jihohi, kananan hukumomi, mazabu da rumfunan zaɓe domin samar da ƙarin goyon bayan jama’a daga ƙasa.
Haka kuma, Kakakin Majalisar ya yaba wa Tinubu bisa rawar da ya taka wajen gina siyasar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda shi ne jagoran kafa CPC, da kuma “girmamawa ta musamman” da aka yi masa bayan rasuwarsa.
Abbas ya ƙara da cewa, gadon siyasar CPC na da tasiri a cikin gwamnatin Tinubu, kasancewar akwai gwamnonin jihohi uku, ministoci da ‘yan majalisa da suka fito daga CPC waɗanda ke rike da muhimman mukamai.

