Wata mata mai sayar da abinci da aka bayyana sunanta kawai da Ammaye ta rasa ranta a hannun gungun matasa a karamar hukumar Mariga ta jihar Neja, bayan zargin yin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Lamarin ya faru ne a Kasuwar Garba da ke cikin yankin, inda shaidu suka ce hatsaniyar ta samo asali daga kauyen Igwama, inda matar – wacce ita ma musulma ce kuma sananniya a wajen mazauna yankin a matsayin mai sayar da abinci – ta yi gardama da wani saurayi da ake cewa ɗan uwanta ne.
Rahotanni sun nuna cewa saurayin ya yi mata barkwanci da cewa yana son auren ta domin “cika Sunna”, abin da ya sa matar ta fadi kalmomi da jama’a suka ɗauka a matsayin ɓatanci, lamarin da ya tayar da hankulan mutane.
An ce an kai karar al’amarin zuwa fadar Hakimin Kasuwar Garba, inda aka yi wa matar tambayoyi, kuma ta maimaita abin da ta fada a baya. Daga nan sai hakimin ya mika ta ga jami’an tsaro domin cigaba da bincike.
Sai dai gungun matasa masu fusata suka nace cewa dole ne a kashe ta nan take. Duk da ƙoƙarin jami’an tsaro na kare rayuwarta, matasan suka rinjaye su, suka jefa mata duwatsu har ta mutu.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, shugaban karamar hukumar Mariga, Abbas Adamu, ya bayyana cewa an shawo kan tashin hankali, kuma an dawo da zaman lafiya a yankin.

