Trends

PSG ta Dauki ‘yar Wasan Super Falcons, Rasheedat Ajibade

Rasheedat Ajibade Sabuwar yar wasan PSG

Tauraruwar kwallon kafa ta Najeriya, Rasheedat Ajibade, ta kammala komawa kungiyar mata ta Paris Saint-Germain (PSG) Féminines inda za ta hadu da takwararta ta kasa, Jennifer Echegini.

Kungiyar PSG ce ta tabbatar da daukar Ajibade a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata. Sanarwar ta ce: “Paris Saint-Germain na farin cikin sanar da isowar ‘yar wasan Najeriya, Rasheedat Busayo Ajibade, wadda ta rattaba hannu kan kwantiragin da zai kare a ranar 30 ga Yuni, 2027.”

Ajibade, wadda ake yi wa lakabi da “Mummy G.O.”, ta bayyana farin cikinta bisa wannan mataki, tana kiran komawarta PSG a matsayin “mataki babba” a ci gaban aikinta.

Ta ce a shafin yanar gizon kulob din: “Ina matukar jin karramawa da na samu damar shiga PSG, daya daga cikin manyan kungiyoyin Turai. Wannan babban mataki ne a rayuwata, kuma zan bayar da duka ƙarfina domin taimaka wa kungiyar ta lashe kofuna tare da zaburar da matasan ‘yan wasa, a Najeriya ko a waje.”

Yan wasan mai shekaru 25 ta iso Paris daga kungiyar Atletico Madrid Femenino ta Sifaniya, inda ta shafe kakanni hudu da rabi tana taka leda.

Ta shiga Atletico a 2021 daga kulob din Avaldsnes IL na Norway, inda ta zura kwallaye 40 a wasa 139. A lokacin zamanta a Madrid, ta taimaka wa kungiyar ta lashe Super Cup na Sifaniya (2021) da kuma Copa de la Reina (2023). A kakar 2024/25, ta zura kwallaye takwas tare da taimakawa wajen cin kwallaye guda uku a wasanni 25.

Zuwan ta PSG ya zo ne makonni kadan bayan ta jagoranci Super Falcons ta lashe Gasarar WAFCON karo na 10, inda aka zabe ta a matsayin ‘Yar Wasan Gasar.

An haifi Ajibade a Lagos a ranar 8 ga Disamba, 1999. Ta wakilci Najeriya a Gasawar Cin Kofin Duniya na Mata 2023, inda tawagar ta kai zagaye na 16.

Haka kuma, ta kasance cikin ‘yan wasan Najeriya da suka buga a Gasawar Olympics ta 2024 a Paris.