Trends

Hatsarin Jirgin Kasa: Bincike ta Bayyana Fasinjoji 6 sun jikkata

Jirgin da ya kauce layi dogo

A kalla fasinjoji shida ne suka jikkata bayan wani jirgin kasa mai tafiya zuwa Kaduna ya yi hatsari a KM 49 tsakanin tashar Kubwa da tashar Asham a ranar Talata, a cewar Hukumar Binciken Tsaro ta Najeriya (NSIB).

A cikin wata sanarwa da Daraktan Harkokin Jama’a da Tallafin Iyali na hukumar ya sanya hannu, an bayyana cewa duk da jikkatar wasu, ba a samu asarar rai ba. Hukumar ta tabbatar da cewa ta tura “go-team” zuwa wajen hatsarin domin tattara shaidu, tattaunawa da masu ruwa da tsaki, tare da fara bincike kan dalilan da suka haddasa hatsarin.

Sanarwar ta ce: “Bayanan da muka samu a halin yanzu sun nuna cewa mutane shida ne suka jikkata, kuma babu wanda ya rasa ransa. An tura tawagar bincike zuwa wurin don tattara shaidu, tattaunawa da masu ruwa da tsaki, da fara bincike kan yanayin da ya jawo hatsarin.

Hukumar na jajanta wa wadanda suka jikkata, tare da nuna goyon bayanta ga dukkan fasinjojin da abin ya shafa. Binciken zai mayar da hankali ne wajen gano abubuwan da kai tsaye da na ainihi da suka haddasa hatsarin, tare da fitar da shawarwari don kaucewa maimaituwa.”

A nasa bangaren, Darakta Janar na NSIB, Kyaftin Alex Badeh, ya ce: “Muna jajantawa matuka ga duk wadanda suka jikkata. Hukumar ta tura kwararrun masu bincike zuwa wurin domin gano hakikanin musabbabin wannan hatsari. Alkawarinmu shi ne tabbatar da tsaron zirga-zirgar jirgin kasa ga ‘yan Najeriya ta hanyar gudanar da bincike mai gaskiya da ‘yanci.”

Hukumar ta kara da cewa za ta rika sanar da jama’a cigaban binciken a kai-a kai.