Wani jirgin fasinja da ke tafiya daga Abuja zuwa Kaduna ya yi hatsarin fashewa daga kan hanya a safiyar Talata, lamarin da ya jefa fasinjoji da iyalansu cikin tsananin firgici.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Kaduna jim kaɗan bayan jirgin ya bar Abuja da misalin ƙarfe 11 na safe, yana kan hanyarsa zuwa Kaduna.
Wani fasinja da ke cikin jirgin ya bayyana cewa yanayin ya kasance cike da rudani, inda mutane ke ta neman mafaka cikin tsoro da rikicewa.
Har yanzu ba a bayyana ainihin abin da ya haddasa hatsarin ba, kuma babu wata tabbatacciyar sanarwa kan ko akwai raunana ko mace-mace.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa an tura sojoji zuwa wurin domin taimaka wa wajen fitar da fasinjojin da suka makale.
Har zuwa yanzu, hukumar Nigerian Railway Corporation (NRC) ba ta fitar da wata sanarwa ba game da lamarin.
Za mu kawo karin bayani…



