PSG ta Dauki ‘yar Wasan Super Falcons, Rasheedat Ajibade
Tauraruwar kwallon kafa ta Najeriya, Rasheedat Ajibade, ta kammala komawa kungiyar mata ta Paris Saint-Germain (PSG) Féminines inda za ta hadu da takwararta ta kasa, Jennifer Echegini. Kungiyar PSG ce ta tabbatar da daukar Ajibade a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata. Sanarwar ta ce: “Paris Saint-Germain na farin cikin sanar da isowar…



