Rundunar Nigerian Television Authority (NTA) ta bayyana cewa, zuwa ranar 16 ga watan Agusta, 2025, ambaliyar ruwa ta shafi jihohi 19 a fadin Najeriya, inda ta yi sanadin mutuwar akalla mutum 165 tare da raba dubban mutane da muhallansu.
A cewar rahoton da NTA ta wallafa a shafinta na X (Twitter), wannan masifa ta jawo mummunar illa, inda aka tattara alkaluma kamar haka: “119,000 sun shiga halin ƙunci, 165 sun mutu, 82 sun ɓace, 138 sun ji rauni, 43,936 sun rasa matsuguninsu.”
Baya ga haka, ambaliyar ta lalata ko ta jawo wa gidaje 8,594 da gonaki 8,278 a kananan hukumomi 43 barna, lamarin da ya ƙara tsananta matsalar rashin matsuguni da kuma ƙarancin abinci a ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa mata da yara sun fi fuskantar matsalar, inda aka tabbatar da cewa 53,314 yara, 36,573 mata, 24,600 maza, 5,304 tsofaffi, da 1,863 masu nakasa suka shiga cikin mawuyacin hali.
Jihohin da suka fi shan mummunar illa sun haɗa da Imo, Rivers, Abia, Borno da Kaduna, yayin da sauran da abin ya shafa suka haɗa da Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Borno, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kogi, Kwara, Neja, Ondo, Rivers, Sokoto da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).
Hakan ya sa hukumomi da ƙungiyoyin agaji ke yin kira da gaggawa don kawo taimako, ciki har da samar da abinci, magunguna, wuraren zama na wucin gadi da kuma tallafi ga iyalan da suka rasa matsuguninsu.
Masana sun yi gargaɗi cewa, da yake damina na ci gaba, al’umman da ke zaune a bakin koguna da wuraren da ke kasa ƙwarai har yanzu suna cikin haɗari. Sun jaddada muhimmancin inganta tsarin gargadi na wuri-wuri da kuma haɗin kai wajen bada agajin gaggawa don rage yawan asarar rayuka.
Source NTA



