Gwamnatin Tarayya ta bayyana damuwa kan wani al’amari mai tayar da hankali: kashi 15 cikin 100 na ’yan mata ’yan Najeriya masu shekaru tsakanin 15 zuwa 19 ko dai suna da ciki ne ko kuma sun riga sun haihu. Wannan ya nuna gaggawar bukatar magance matsalolin lafiyar haihuwa na matasa da kuma bambancin jinsi.
Ministar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a, Imaan Sulaiman-Ibrahim, ce ta bayyana wannan a lokacin kaddamar da manhajar farko ta ƙasa kan tsabtace jinin al’ada da kula da shi (National Policy on Menstrual Health and Hygiene Management – MHHM).
Ministar, wacce sakatariyar dindindin ta ma’aikatar, Maryam Keshinro, ta wakilta, ta kuma bayyana cewa sama da mata da ’yan mata miliyan 7.3 a Najeriya na fama da rashin wadataccen abinci (undernutrition), yayin da kashi 55% daga cikinsu ke fama da cutar rashin jini (anaemia). Ta danganta wannan matsala da rashin tsafta a lokacin al’ada da kuma ƙarancin samun kayan tsaftar al’ada a farashi mai sauƙi.
Sulaiman-Ibrahim ta bayyana sabon tsarin a matsayin “muƙamin tarihi,” inda ta jaddada cewa ya zama dole a ɗauki jinin al’ada a matsayin al’ada ta dabi’a, ba abin kunya ko tozarci ba, balle ma ya zama dalilin wahala ga tattalin arzikin mata da ’yan mata.
Ta kuma yaba wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu bisa amincewa da cire haraji daga kayan tsaftar al’ada, tana cewa hakan babban mataki ne wajen magance matsalolin kiwon lafiyar jama’a da na bambancin jinsi.
“Ya zama wajibi mu tabbatar cewa jinin al’ada bai zama shamaki ga haƙƙi, damar ci gaba, ko walwalar kowace mace ko yarinya ba,” in ji ta.
Haka kuma, Fifi Ogbondeminu, wakiliyar rikon kwarya ta ƙungiyar Population Services International (PSI) Nigeria, ta goyi bayan matsayin ministar, inda ta ce ya kamata a ɗauki lafiyar al’ada a matsayin batun haƙƙin ɗan adam da ci gaban al’umma.
Ta bayyana sabon tsarin a matsayin muhimmin mataki don ganin an magance batun al’ada cikin “mutunci, tausayi da gaggawa,” tana mai jaddada cewa warware matsalolin lafiyar al’ada muhimmin mataki ne wajen cimma daidaiton jinsi da kuma inganta rayuwar miliyoyin mata da ’yan mata a Najeriya.



