Muslim Public Affairs Centre (MPAC), Najeriya, ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta shiga cikin shari’ar tarihi da ƙasar Afirka ta Kudu ta shigar da Isra’ila a gaban Kotun Ƙasa da Ƙasa (ICJ).
Shugaban MPAC, Disu Kamor, a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa wannan mataki na da matuƙar muhimmanci, duba da yadda duniya ke ci gaba da kallo cikin firgici da bakin ciki irin ta’asar da Isra’ila ke yi wa al’ummar Palasɗinu.
Ya ce wannan ta’asa tana ɗauke da dukkan alamu na kisan kare-dangi, laifukan yaƙi, da kuma laifuka kan bil’adama, inda ya kawo misalai da dama na yadda Isra’ila ke kai hare-haren bama-bamai ba tare da bambance fararen hula ba, kai tsaye ga asibitoci, makarantu, sansanonin ’yan gudun hijira, ma’aikatan jin kai, da kuma hana mata da yara abinci ta hanyar yunwa da gangan.
Kamor ya yaba wa Afirka ta Kudu bisa jarumta da jajircewa wajen kalubalantar Isra’ila a ICJ ta hanyar amfani da yarjejeniyar Genocide, wacce Najeriya ma ta sanya hannu a kanta.
“Wannan lokaci ne na gaskiya ga ƙasashen duniya, kuma Najeriya ba za ta iya yin shiru ko nuna halin ko in kula ba. Najeriya ta dade tana kafa tarihi a matsayin mai kare adalci, mai goyon bayan yaƙin kawar da wariyar launin fata (apartheid) da kuma kare ’yancin talakawa a duniya. Wannan gado ne da ya wajabta wa gwamnati ta yi aiki yanzu ta tsaya tsayin daka tare da Afirka ta Kudu da sauran ƙasashen da ke neman a ɗaura wa Isra’ila alhakin abin da take aikatawa,” in ji shi.
Ya gargadi cewa rashin shiga cikin wannan yunkuri zai zama cin amana ga ka’idojin adalci, jin kai, da hadin kai da Najeriya ta saba ikirari a kansu.
Saboda haka, MPAC ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatin Najeriya da su shiga wannan shari’a a matsayin mai ƙara tare da Afirka ta Kudu, domin ƙara nauyin doka da ɗabi’a a gaban kotun.
Ƙungiyar ta kuma nemi Najeriya ta dauki matsaya mai ƙarfi a gaban Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran cibiyoyin duniya, ta hanyar buƙatar kawo ƙarshen wannan ta’asa a kan Palasɗinu, tare da nuna jagoranci a nahiyar Afirka wajen kare adalci, zaman lafiya da rayuwar marasa ƙarfi.
“Tarihi ba zai taɓa yi wa ƙasashen da suka zabi yin shiru adalci ba. Najeriya kada ta kasance cikin waɗannan ƙasashe,” in ji Kamor.



