Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bayyana rashin amincewarta da shirin ƙara albashin manyan ’yan siyasa a Najeriya, tana mai kiran wannan yunkuri “mara hankali” da kuma “cin fuskar talakawan ƙasar nan”.
A cewar ADC, Shirin da Hukumar Rabon Kuɗaɗe da Sake Tsara Albashi (RMAFC) ke shirin aiwatarwa zai bai wa shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, gwamnonin jihohi da sauran manyan jami’an gwamnati karin albashi mai yawa a daidai lokacin da miliyoyin ’yan Najeriya ke fama da hauhawar farashin kaya, tashin farashin mai, da kuma ƙarancin mafi ƙarancin albashi.
Mallam Bolaji Abdullahi, mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, duk da cewa RMAFC na da hurumin doka na duba albashin masu rike da mukaman siyasa lokaci zuwa lokaci, ba shi da ma’ana a aiwatar da hakan a wannan lokaci da al’umma ke cikin tsananin wahala.
Sanarwar ta ci gaba da cewa:
“Maimakon a ƙara albashin shugabanni, gwamnati ta mai da hankali wajen ƙara mafi ƙarancin albashi wanda yake N70,000 a wata, wanda ma ba a cika biyan shi ba a yawancin wurare. Wannan adadi kuma ya riga ya lalace saboda hauhawar farashin kayayyaki da gwamnatin APC ta jefa ƙasa a ciki. Yayin da ’yan siyasa ke samun kuɗaɗe daga alawus-alawus da wasu boyayyun kuɗaɗe, talakawa kuwa ba su da wata kariya daga tsadar rayuwa.”
ADC ta ce bayanin shugaban RMAFC cewa albashin yanzu “ya tsufa kuma bai dace ba” ba shi da tushe, domin duk da cewa albashin a rubuce bai yi yawa ba, akwai tarin wasu kuɗaɗe na musamman da ke sa ’yan siyasa rayuwa cikin alfarma.
Jam’iyyar ta yi gargadi cewa aiwatar da wannan shiri zai nuna gwamnati ta rasa alaka da hakikanin halin da talakawan Najeriya ke ciki.
“Ba za a ce gwamnati na neman hadin kan talakawa wajen jure wahalhalu, yayin da shugabanni ke ƙoƙarin sauƙaƙa rayuwarsu ta alatu da karin albashi ba. Wannan cin mutunci ne ga al’umma,” in ji sanarwar.
ADC ta yi kira da a dakatar da wannan shiri nan take, tana mai jaddada cewa bai kamata gwamnati ta ƙara albashin ’yan siyasa ba sai dai ta tabbatar da cewa albashin ma’aikatan gwamnati ya kai matakin da ya dace da tsadar rayuwa, sannan ta inganta shirye-shiryen jinƙai don tallafa wa mafi raunin al’umma.
Mallam Bolaji Abdullahi
Mai Magana da Yawun Jam’iyyar na Ƙasa
African Democratic Congress



