A wani mataki da aka ɗauka domin rage wa ’yan Najeriya masu fama da cutar koda nauyin kuɗin jinya, Shugaba Bola Tinubu ya yi umarnin rage kuɗin yin wanke jini (dialysis) a asibitocin tarayya daga Naira 50,000 zuwa Naira 12,000 kacal.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Daniel Bwala, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin ta shafinsa na X, inda ya ce wannan tallafin zai fara ne a manyan asibitoci goma na gwamnati, ciki har da cibiyoyin kula da lafiya na tarayya da asibitocin koyarwa a birane kamar Legas, Abuja, Ibadan, Maiduguri, Owerri da Kalabar.
Bwala ya ƙara da cewa ana da shirin faɗaɗa wannan tsari zuwa ƙarin asibitoci a faɗin ƙasar nan kafin ƙarshen shekara domin tabbatar da cewa mafi yawan ’yan ƙasa za su iya samun wannan kulawa cikin sauƙi. Ya jaddada cewa wannan matakin wani ɓangare ne na jajircewar Tinubu wajen tabbatar da cewa lafiyar ’yan Najeriya ta inganta, musamman ma talakawa da marasa galihu.
A cewar Bwala: “Wannan ci gaban zai kawo sauƙi ga dubban ’yan Najeriya da ke fama da cututtukan koda, waɗanda da dama ba su da ƙarfin biya kuɗin yin wanke jini. Za a ƙara wasu cibiyoyin kula da lafiya da asibitocin koyarwa kafin ƙarshen shekara domin faɗaɗa damar samun wannan hidima a duk faɗin ƙasar.”
Wannan dai ba shi ne karo na farko da gwamnati ke aiwatar da sauye-sauyen kiwon lafiya a ƙarƙashin shirin “Renewed Hope Agenda” na shugaban ƙasa ba. A bara, Tinubu ya amince da bayar da tiyatar haihuwa ta hanyar C-section kyauta ga mata masu juna biyu a asibitocin tarayya domin rage mace-macen mata masu ciki da inganta kulawar uwa da jariri.
Waɗannan manufofin guda biyu suna nuna cewa gwamnatin Tinubu ta daɗe da aniyar ganin cewa babu wani ɗan Najeriya da za a hana shi samun kulawar lafiya saboda ƙarancin kuɗi.







