Tinubu na Kawo kwanciyar Hankali da Ci Gaba a Najeriya – Okowa

Ifeanyi Okowa Tsohon Gwamnan Jihar Delta

Tsohon Gwamnan Jihar Delta kuma mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Ifeanyi Okowa, ya ce Shugaba Bola Tinubu na dawo da kwanciyar hankali da bege a Najeriya.

Okowa ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Abuja, yayin taron ƙasa da ƙungiyar Integrity Group of Nigeria (IGN) ta shirya mai taken “Renew Hope Agenda through Continuity.”

An wakilci Okowa a wajen taron da tsohon mai ba shi shawara kan harkokin majalisar tarayya da alaƙar gwamnati, Pascal Adigwe. Ya jaddada bukatar Tinubu ya ci gaba da zama a ofis domin ’yan ƙasa su ci gaba da amfana daga manufofinsa.

Ya bayyana Tinubu a matsayin “shugaban da ke aiwatarwa,” wanda ya ɗauki alhakin shugabanci, sabanin wasu shugabannin da suka gabata.

Okowa ya ce: “Shawarwarin Tinubu na iya zama masu tsauri ko wuya, amma suna haifar da sakamako mai kyau. Tinubu na kawo kwanciyar hankali. Ya dawo da bege. Ya ɗauki ƙalubale kai tsaye. Ba ya jingina matsaloli ga shugabannin baya ko yadda aka tafiyar da mulki a da. Ya yi wa Najeriya alkawari cewa zai hau mulki ya ɗauki alhaki, kuma hakan ne yake yi yanzu.”

Tsohon gwamnan ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Tinubu a tazarcensa na shekarar 2027, yana mai cewa shugaban ƙasa ya nuna ƙudurinsa na ɗaukar alhakin tafiyar da ƙasar.

Ya ce: “Mun zo ba da kaya ba, sai dai da arziki don mu inganta abin da ka gina. Mun zo da ƙwarewarmu, da sanin muhallin ƙasa, da ƙauna, da albarkatun da za su inganta rayuwar jama’a.”

Okowa ya bukaci kungiyoyin goyon baya su fara shirin tabbatar da nasarar Tinubu a 2027, yana mai cewa ya cancanci hakan.

Tun da farko, mai shirya taron kuma shugaban ƙasa na IGN, Dr. Oke Idawene, ya bayyana cewa Tinubu ya hau mulki cikin shiri, kuma yana aiki don bunƙasar ƙasa.

Ya ce: “Saƙon wannan rana shi ne kada mu sake bari waɗanda ke satar arzikin Najeriya su sake shugabantar mu.”

Idawene ya ƙara da cewa dalibai yanzu suna samun damar karɓar rance, sannan tsaro yana inganta. Ya kuma ce gwamnonin jam’iyyar APC na shirin tabbatar da nasarar Tinubu a 2027 bisa ga hazakarsa.

Haka nan, Sanata Binta Garba ta bayyana cewa lokacin da Tinubu ya hau mulki abubuwa ba su tafiya daidai a ƙasa, amma ya samu damar gyara su. Ta nuna fatan cewa a 2027 za a ci gaba da shirin Renewed Hope, tana mai cewa “ci gaba shi ne zai inganta Najeriya.”

Tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen, ta kira ’yan Najeriya da su yi wa Tinubu addu’a tare da ba shi goyon baya da ake buƙata don ya inganta ƙasar. Ta ce alamu na ci gaba sun fara bayyana, tana misalta nasarorin jam’iyyar APC a zaɓen cike gurbi da kuma ’yan mata ’yan Najeriya da suka lashe kyaututtuka a fannoni daban-daban na wasanni.

Shugabar Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Akure (FUTA), Farfesa Nora Daduut, ta yaba wa ƙungiyar saboda shirya taron ƙasa. A matsayinta na “uwa ta musamman” a wajen taron, ta umurci mambobin ƙungiyar, musamman mata, da su ci gaba da yada saƙon shirin Renewed Hope.