Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja a ranar Alhamis domin yin ziyarar aiki zuwa kasashen Japan da Brazil.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, an bayyana cewa shugaban zai tsaya a Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa, kafin ya wuce Japan.
A Japan, Shugaba Tinubu zai halarci taron Ninth Tokyo International Conference on African Development (TICAD9) da za a gudanar a birnin Yokohama daga ranar 20 zuwa 22 ga watan Agusta. Taken taron na bana shi ne “Haɗa Hannu Wajen Kirkirar Ingantattun Hanyoyin Cigaba Tare da Afirka”.
Taron zai mai da hankali kan sauya fasalin tattalin arzikin Afirka da inganta yanayin kasuwanci da cibiyoyi ta hanyar saka hannun jari na masu zaman kansu da kirkire-kirkire. Haka kuma, zai tallafa wajen gina al’umma mai ɗorewa da jure wa kalubale, tare da tabbatar da tsaro, zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Baya ga halartar zaman taro, shugaban Najeriya zai gudanar da ganawar bangarori biyu da wasu shugabanni, sannan kuma ya gana da shugabannin manyan kamfanonin Japan masu zuba jari a Najeriya.
TICAD an fara shi ne a shekarar 1993 ta gwamnatin Japan, tare da haɗin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya, UNDP, Hukumar Tarayyar Afirka, da kuma Babban Bankin Duniya. Ana gudanar da shi duk bayan shekaru uku a Japan ko a Afirka. Taron na baya-bayan nan ya gudana ne a watan Agustan 2022 a kasar Tunisia.
Bayan kammala taron TICAD9, Shugaba Tinubu zai tashi zuwa birnin Brasilia, babban birnin tarayyar Brazil, a ziyarar kwanaki biyu daga Lahadi 24 zuwa Litinin 25 ga watan Agusta, bisa gayyatar shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva.
A Brazil, shugaban zai yi ganawar bangarori biyu da shugaban kasar Brazil, sannan ya halarci taron kasuwanci tare da ‘yan kasuwar Brazil. Tawagarsa, wacce ta kunshi ministoci da manyan jami’an gwamnati, za ta tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa da rattaba hannu kan yarjejeniyoyi da takardun fahimtar juna (MoUs) tare da gwamnatin Brazil.

