Rikicin Filin Jigir: IGP Ya Umarci a Binciki KWAM 1

KWAM 1 photo credit, Punch

Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya ba da umarni ga rundunar ‘yan sanda da ke filin jirgin sama da ta gudanar da bincike kan fitaccen mawaƙin Fuji, Wasiu Ayinde (Kwam 1), biyo bayan saɓani da ya samu da wasu jami’an filin jirgi.

Rahotanni sun bayyana cewa mawaƙin ya aikata abin da aka bayyana a matsayin “halin rashin ladabi” a makon da ya gabata, inda ake zargin ya hana gudanar da aikin jirgi cikin tsaro, lamarin da ya saba wa dokokin sufurin jiragen sama na Najeriya.

Da yake mayar da martani kan tambayoyin Daily Trust, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda, Olumuyiwa Adejobi, ya ce shugaban ‘yan sandan ya bayar da umarnin fara bincike nan take kan lamarin.

Adejobi, wanda shi ne Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, ya bayyana cewa IGP na son jami’ai su gano ainihin abubuwan da suka jawo wannan mummunan lamari tare da tabbatar da adalci.

Ya ƙara da cewa IGP ya yi gaggawar bayar da wannan umarni ne bayan shugabancin rundunar ya karɓi ƙorafi na musamman daga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA).

Cikakkun bayanai za su biyo baya…