Hukumar National Youth Service Corps (NYSC) ta bayyana dalilin da ya sa ta janye takardar kammala aikin yi wa kasa (discharge certificate) na Rita Uguamaye, wadda ta yi fice a shafukan sada zumunta bayan ta yi suka ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan halin da kasa ke ciki.
Uguamaye ta zama abin magana ne bayan ta zargi gwamnatin tarayya da jinkirin biyan karin alawus ga ‘yan aikin yi wa kasa, duk da cewa gwamnati ta sanar da karin daga N33,000 zuwa N77,000. A cikin wani faifan bidiyo da ya bazu, Uguamaye ta ce jinkirin biyan kudin ya jefa abokan aikinta cikin mawuyacin hali.
Maganarta ta haifar da ce-ce-ku-ce, inda wasu suka yabawa jarumtarta, yayin da wasu kuma suka yi zargin cewa ba daidai ba ne ga ‘yar aikin yi wa kasa ta yi irin wannan suka ga gwamnati ko hukumar.
An ruwaito cewa an tsawaita shekarar aikin yi wa kasa na Rita a matsayin hukunci, kafin daga bisani a yada labarin cewa an janye mata takardar kammala aiki, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.
A martanin da ta bayar kan wannan batu, hukumar NYSC ta fitar da sanarwa tana fayyace lamarin:
“Hukumar NYSC tana son ta bayyana gaskiya kan rahotannin da ke yawo a shafukan sada zumunta game da Corps Member Ushie Rita Uguamaye, mai lambar State Code LA/24B/8325.
“Akasin yadda ake yadawa cewa an hana ta takardar kammala aiki saboda ta yi suka ga gwamnati, wannan batu ba shi da tushe balle makama. Rita na daga cikin ‘yan aikin yi wa kasa 131 da aka dakatar da takardun kammalawa saboda dalilan ladabtarwa na gaskiya. Musamman, an tsawaita shekarar aikinta da watanni biyu saboda rashin halartar tantancewar biometric na watan Afrilu 2025, hukuncin da ya dace da kundin tsarin mulkin NYSC.
“Ya kamata a lura cewa wannan tsawaita wa’adi al’ada ce a hukumar, ba kuma ita kadai abin ya shafa ba. Ka’idar adalci da daidaito kawai aka bi a wannan lamari.
“NYSC tana kira ga jama’a da su fahimci cewa tsawaita aikin yi wa kasa saboda rashin bin doka al’ada ce tun da dadewa a cikin hukumar, don haka bai kamata a siyasantar da shi ba.
“Hukumar NYSC za ta ci gaba da gudanar da aikinta bisa tanadin kundin tsarin mulkin kasa. Nigeria namu ce; Nigeria muke yi wa hidima.”
