Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (Abuja Electricity Distribution Company – AEDC) ya sanar da katsewar wutar lantarki a wasu sassan Babban Birnin Tarayya Abuja da Jihar Kogi.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a cikin sanarwa biyu daban-daban da ya wallafa a shafinsa na X a ranakun Asabar da Lahadi.
A cewar AEDC, wuraren da abin ya shafa a Abuja sun hada da: Zulu Community, Eco Bank, Guardian Newspaper da kewaye; haka kuma ENL, Paradise Estate, FHA Guzape, Efab Classic Estate, Metro City Estate, Sticks & Stones, Yayala Estate, Trademore Estate, Choos Estate, Maxcare Plaza, Faith Plaza, da Sunflower Plaza.
Sauran wuraren sun hada da Erifu Estate, DME Estate, Greenpath School, Earth Point Estate, Sunnyvale Estate, Brains & Hammer 1, 2, 4, Hunters Garden, Ecofitness, Brains & Hammer 3 Apo, Bamaga Tukur Street, Eye Clinic, Best Way Hotel, Franca Afegbua Crescent, Zone C, Defence College, Checkin Hotel, Abba Kyari Street, Adeyemi Adesoji Street, Start Right School, Zone E Extension, Idu, Karmo, Citec Mbora, Airport Road, Nile University, Base University, Karimajiji, Kuchingoro, da kewaye.
AEDC ta bayyana cewa matsalar ta faru ne sakamakon wata ila ta fasaha a wasu sassan Abuja, wanda ya haifar da katsewar wutar lantarki a yankunan da aka lissafa.










