Yakin Gaza: ‘Pele na Falasɗinu’ Suleiman al-Obeid Ya Rasu Yayi Harin Isra’ila

Suleiman al- Obied Pelen Kasar Palasdinu

Ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙungiyar ƙasa ta Falasɗinu, Suleiman al-Obeid, ya rasu sakamakon harin Isra’ila kan masu neman tallafi a Gaza.

Al-Obeid, mai shekara 41, ya rasu ne a ranar Laraba lokacin da dakarun Isra’ila suka kai hari kan jama’ar da ke jiran tallafi a kusa da cibiyar rarraba kayan agaji a kudancin Gaza, in ji Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Falasɗinu.

Ana yi masa laƙabi da “Pele na ƙwallon ƙafa ta Falasɗinu” – bayan fitaccen ɗan wasan Brazil, Pele, wanda ake ɗauka ɗaya daga cikin mafiya hazaka a tarihin ƙwallon ƙafa.

A tsawon shekarunsa a filin wasa, wannan ɗan wasa daga Gaza ya zura fiye da kwallaye 100, lamarin da ya sanya shi cikin fitattun taurarin ƙwallon ƙafa na Falasɗinu.

Tare da sanar da rasuwarsa, Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Falasɗinu ta ce:
“Tsohon ɗan wasan ƙasa kuma tauraron ƙungiyar Khadamat al-Shati, Suleiman al-Obeid, ya yi shahada bayan [dakarun] mamayar Isra’ila sun kai hari kan masu jiran tallafin jin ƙai a kudancin zirin Gaza a ranar Laraba.”

Da rasuwar al-Obeid, adadin ‘yan wasa da iyalansu da aka kashe tun bayan fara yakin Isra’ila a Gaza ya kai 662. Adadin wadanda suka rasu da suka shafi ƙwallon ƙafa a Gaza yanzu ya kai 321, ciki har da ‘yan wasa, masu horarwa, masu gudanarwa, alkalai, da shugabannin kulob.

Tsohon tauraron ya fara wasan sa da kulob din Khadamat al-Shati a Gaza, kafin daga bisani ya koma kungiyar Al-Amari Youth Center da ke cikin yankin Yammacin Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

A matakin kasa da kasa, al-Obeid ya buga wasanni 24 tare da ƙungiyar ƙasa ta Falasɗinu (Al-Fida’i), inda ya zura kwallaye biyu. Sanannen kwallonsa ya kasance na “scissor kick” da ya zura wa ƙungiyar ƙasa ta Yemen a gasar West Asian Football Federation Championship ta shekarar 2010.

Ya bar mata ɗaya da ‘ya’ya biyar.

Fiye da Falasɗinu 1,300 ne aka kashe a kusa da wuraren rarraba tallafi da Ƙungiyar Gaza Humanitarian Foundation ke gudanarwa tun bayan fara ayyukanta a ƙarshen watan Mayu.

A kalla mutum 18 ne suka rasu a ranar Laraba yayin neman tallafi, in ji majiyoyin lafiya ga Al Jazeera, a yayin da yunwa ke kara ta’azzara a Gaza yayin da Isra’ila ke ci gaba da sanya tsauraran matakai kan shigar kayan agaji.

Asibitocin Gaza kuma sun tabbatar da karin mace-mace hudu a cikin sa’o’i 24 da suka gabata sakamakon yunwa da rashin abinci mai gina jiki, a cewar ma’aikatar lafiya ta yankin, lamarin da ya kai adadin mace-mace sanadiyyar yunwa zuwa 197, ciki har da yara 96, tun bayan fara yakin Isra’ila kan Gaza a watan Oktoba 2023. Yawancin mutuwar ta faru ne a ‘yan makonnin nan.