Audu Ogbeh Tsohon Minista Kuma Tsohon Shugaban PDP Ya Rasu

Audu Ogbe Tsohon Ministan noma

Audu Ogbeh, tsohon shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da kuma tsohon ministan noma daga 2015 zuwa 2019, ya rasu.

Ya rasu ne a ranar Asabar, 9 ga watan Agusta, yana da shekaru 78.

A cikin wata sanarwa, iyalansa sun bayyana cewa:

“Ya rabu da mu cikin salama, yana barin tarihi na gaskiya, hidima da jajircewa ga kasarmu da al’ummarmu. Muna samun kwanciyar hankali da rayukan da ya taba da kuma kyawawan misalan da ya kafa.”

Sun ce za a sanar da cikakkun bayanan shirye-shiryen jana’iza nan gaba, tare da gode wa abokai, ‘yan uwa da masu yi musu ta’aziyya bisa addu’o’i da goyon bayan da suka nuna a wannan lokaci.

“Za mu yaba idan aka bar mu cikin sirri a wannan lokaci yayin da muke jimamin rashin uban gidajenmu,” in ji sanarwar.

Ogbeh ya rike mukamin shugaban PDP daga 2001 zuwa 2005, sannan ya yi minista a zamanin marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Haka kuma, ya taba zama ministan sadarwa na tarayya daga 1982 zuwa 1983 a mulkin Shehu Shagari.

Ogbeh ya fara siyasa a 1979, inda ya zama mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Benue har zuwa 1982.