AIBEN Property Zai Dauki Nauyin Gasar Kwallon Kafa ta NUJ FCT karo na 4

Shugaban NUJ FCT Grace Ike tare da Shugaban AIBEN Property Mista Andy Elerewe

Kamfanin AIBEN Property, daya daga cikin manyan masu ruwa da tsaki a harkar gidaje a Najeriya, ya sha alwashin daukar nauyin gasar kwallon kafa ta kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ) reshen babban birnin tarayya (FCT) karo na 4, wadda aka tsara gudanarwa a shekarar 2026.

Manajan Darakta kuma Shugaba na AIBEN Property, Mista Andy Elerewe, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar girmamawa da wata tawaga daga NUJ FCT karkashin jagorancin shugabar kungiyar, Ms Grace Ike, ta kai masa a ranar Alhamis a Abuja.

Mista Elerewe ya yabawa NUJ bisa irin wannan gagarumin tsari na amfani da wasanni, musamman kwallon kafa, a matsayin hanya ta hada kan ‘yan jarida, hukumomin tsaro, bangarorin gwamnati da masu zaman kansu. Ya bayyana cewa hadin kai tsakanin AIBEN da kafafen yada labarai ya kara karfafa zumunci da gasa mai tsafta.

“A matsayinmu na masu daukar nauyin wannan gasa, AIBEN za ta samar da filinta na wasanni — Maralago Sports Complex da ke kan hanyar Kubwa — a matsayin filin da za a yi gasar karo na 4. Za mu ci gaba da kasancewa manyan masu daukar nauyi na gasar,” in ji shi.

Ya kara da cewa gasar ta wuce wasan kwallon kafa kawai, domin tana bai wa mahalarta damar gina alaka, kara fahimta da hadin gwiwa tsakanin ‘yan jarida da sauran hukumomin da ke shiga gasar. Ya tabbatar da cewa kamfaninsu zai ci gaba da marawa shirye-shiryen da ke karfafa hadin kai da ci gaban al’umma baya.

A yayin ziyarar, NUJ FCT ta mika wa Mista Elerewe kayayyakin tallata gasar ciki har da takardun talla, tutoci da rigar wasanni ta musamman mai lamba 10. Shugaban AIBEN ya nuna farin cikinsa da gasar tare da bayyana aniyarsa ta taka leda a gasar.

Ms Grace Ike ta bayyana godiya ga AIBEN bisa goyon bayanta tun daga farkon gasar, lokacin da kungiyar Correspondents’ Chapel ke shirya ta kadai. Ta ce yanzu da Majalisar NUJ ta dauki gasar, an samu karin kima da tasiri.

“Wasan kwallon kafa yare ne da kowa ke fahimta. Wannan gasa ta zama wata babbar hanya da ke hade ‘yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki daga bangarori daban-daban,” in ji ta.

An shirya gudanar da gasar karo na 3 daga 18 zuwa 23 ga watan Agusta, 2025, a filin kwallo na Area 3 da kuma na Area 10, duk a kusa da Old Parade Ground da ke Abuja.

Kungiyoyin da za su shiga gasar sun hada da: AIBEN Properties, Hukumar Kiyaye Hadurra (FRSC), Rundunar ‘Yan Sanda (NPF), Hukumar Shige da Fice (NIS), Hukumar Kwastam (NCS), Kotun Tarayya (FHC), da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA).

Sauran su ne: Kungiyar ‘Yan Jarida Masu Labaran Wasanni (SWAN), Rundunar Sojin Sama (NAF), da Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ).

Za a gudanar da bikin kintsa kungiyoyi da taron manema labarai na gasar a ranar 12 ga watan Agusta, 2025, da misalin karfe 10 na safe a sakatariyar NUJ FCT da ke Utako.

Tun lokacin da aka fara gasar a 2023 da 2024 karkashin jagorancin NUJ Correspondents’ Chapel, Hukumar FRSC ce ta lashe kofin sau biyu a jere.