Trends

Karin Bayani: WAEC Ta Magance Matsalar Fasaha, Ta Bude Shafin Duba Sakamako

Hukumar Shirya Jarabawar Yammacin Afirka (WAEC) ta tabbatar da cewa ta warware matsalolin fasaha da suka shafi wasu daga cikin sakamakon jarabawar WASSCE ta shekarar 2025 da aka fitar kwanan nan.

WAEC ta bukaci dukkan ɗaliban da suka riga suka duba sakamakonsu da su sake dubawa.

A cikin wata sanarwa da Sashen Harkokin Jama’a na hukumar ya fitar a ranar Alhamis, an bayyana cewa matsalolin fasaha sun shafi darussan Lissafi, Turanci, Ilmin Halittu (Biology), da tattalin arziki.

Wannan tangarda ta fito fili ne bayan samun koke-koke daga ɗalibai da wasu masu ruwa da tsaki, lamarin da ya tilasta hukumar gudanar da cikakken bincike a cikin gida.

WAEC ta danganta matsalar da wani sabon tsari da aka bullo da shi don yaki da magudin jarabawa mai suna paper serialisation. Hukumar ta ce wannan tsari yana daidai da ƙa’idodin duniya kuma ana amfani da shi a wasu ƙasashe, amma a wannan karo ya haddasa matsaloli a lokacin sarrafa sakamakon wasu darussa.

Saboda haka, an dakatar da damar duba sakamakon jarabawar WASSCE ta 2025 ga daliban makaranta (School Candidates) a shafin hukumar na ɗan lokaci. WAEC ta sanar da cewa yanzu ta gyara matsalar kuma ta shawarci ɗalibai su sake duba sakamakonsu bayan awa 24.

Hukumar ta bayar da hakuri bisa wannan matsala da ta jawo damuwa ga jama’a da ɗalibai, tare da godewa bisa hakuri da fahimtar da suka nuna.

WAEC ta sake jaddada kudurinta na tabbatar da adalci da ƙwarewa, tana mai cewa za ta ci gaba da ba da ingantacciyar hidima ga duka masu ruwa da tsaki.