Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta bayyana cewa za a fara da adadin naira miliyan 8.5 a matsayin ajiyar farko na aikin Hajjin shekarar 2026, yayin da ake ci gaba da tattaunawa da masu ba da sabis a ƙasar Saudiyya.
Wannan sanarwa ta fito ne a yayin wani taron bitar aikin Hajji da aka gudanar a ranar Alhamis a hedkwatar NAHCON da ke Abuja, inda Shugabanni da Sakatarorin Hukomomin Jin Daɗin Alhazai na jihohi suka halarta.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana cewa Najeriya ta ci gaba da rike kujerun alhazanta guda 95,000 daga Masarautar Saudiyya kamar yadda aka samu a shekarar 2025, kuma rabon kujeru ga kowace jiha zai kasance kamar yadda aka tsara a bara.
A cewar wata sanarwa da Fatima Sanda, Shugabar Sashen Hulɗa da Jama’a ta hukumar ta fitar, Farfesa Usman ya jaddada muhimmancin fara shiri da wuri, inda ya ce Najeriya na kokarin samun guraben jirage tun da wuri ta hanyar ci gaba da amfani da kamfanonin jiragen sama guda huɗu da aka yi amfani da su a aikin Hajjin 2025.
Shugaban ya godewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa tallafin da ya baiwa alhazan Najeriya, musamman ta hanyar bada umarni ga kamfanonin jigilar alhazai da su amince da biyan kuɗin tikiti da naira maimakon dala, da kuma janye tsarin babban bankin ƙasa (CBN) da ke tilasta amfani da kati wajen samun kuɗin tafiya na BTA.
Ya bayyana cewa waɗannan matakai sun kare alhazai daga matsin lambar musayar kuɗi da kuma rashin samun damar shiga tsarin dijital.
Taron ya kuma tattauna game da jadawalin aikin Hajji na 2026, ƙalubale na aiki da kuma shawarwari don gyara tsarin. Kwamishinan Ayyuka, Prince Anofiu Elegushi, ya jagoranci muhawara kan harkokin sufuri, yayin da Kwamishinan Tsare-tsare da Bincike, Farfesa Abubakar Yagawal, ya bayyana lokacin da aka tsara don fara shirye-shiryen Hajjin.
A madadin Forum na Sakatarorin Jihohi, Alhaji Idris Almakura daga Jihar Nasarawa ya bukaci ƙarin haɗin gwiwa tsakanin NAHCON da hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi.
An kammala taron da alƙawarin ci gaba da bayar da ƙarin bayani bayan kammala tattaunawa a matakin jihohi. Sakatare na hukumar, Dr. Mustapha Ali, ya godewa mahalarta taron tare da rufe zaman.
A aikin Hajjin 2025, alhazai daga Najeriya sun biya tsakanin Naira miliyan 8.32 zuwa miliyan 8.78, dangane da jiharsu.
