Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), amma yana da niyyar mara baya ga kowanne irin tsari da zai taimaka wajen kifar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga mulki a shekarar 2027.
Yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na tashar Arise News ranar Talata, Lamido ya bayyana APC a matsayin cutar da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.
“Dole mu yanke wannan ciwon da ake kira APC, wanda zan iya kwatanta da cutar sankarau ko ciwon daji (cancer) mataki na hudu. APC ce matsalarmu. Dole ne mu yanke wannan cin hanci da ya zama cuta a Najeriya,” inji Lamido.
Duk da yake ya nuna cewa yana da wasu damuwa kan sabuwar kawancen da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ke jagoranta, ya ce:
“Ban kasance a ciki ba, amma zan iya mara wa duk wani tsari da kowanne suna, musamman a yanzu, domin dawo da martabar Najeriya. Ba wai batun Tinubu bane, amma batun APC ne.”
Lamido ya bayyana cewa tun daga shekarar 2015 da APC ta hau mulki, ba ta tabuka abin a zo a gani ba, yana mai cewa ra’ayin kafa kawance a matsayin hanyar karfafa dimokuradiyya kyakkyawan ra’ayi ne.
Sai dai ya bayyana shakku kan tsayin daka da niyyar wasu daga cikin fitattun shugabannin adawa da ke jagorantar kokarin kawar da shugaban kasa Bola Tinubu da APC daga mulki. Ya bukaci su “rage gudu” su gina jam’iyya mai karfi tare da hada kan ‘yan Najeriya bisa manyan batutuwan kasa maimakon mayar da hankali kan mutum daya.
“Ina ganin ana yin sauri fiye da kima. Masu tsere da yawa ne a cikin wannan tafiya. Ina ganin ya kamata su rage gudu su zauna su nazarci lamarin sosai, su fito da tsari na kawance da zai hada kan kasa, kawance na sha’anin kasa, wanda zai iya karya wannan cuta da ake kira APC.”
Lamido, wanda ya rike mukamin Ministan Harkokin Waje daga 1999 zuwa 2003, ya sake jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar PDP duk da rikice-rikicen cikin gida da jam’iyyar ke fama da su.
“Idan rikici ya taso, guduwa ba mafita ba ce. Dole mutum ya tsaya ya fafata da bakin kokarinsa, domin ganin mafarkin ‘yan gabanmu na Najeriya ya tabbata –
ko a cikin jam’iyya ko a wajen ta,” inji shi.
Daga cikin manyan ‘yan siyasar da suka rasa matsayi ko tasiri a jam’iyyunsu akwai tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na PDP a 2023, Atiku Abubakar; tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai; tsohon Gwamnan Osun kuma tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola; tsohon Gwamnan Jihar Ribas kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, wanda nan take aka ayyana shi a matsayin shugaba na kasa na sabon tsari.
Haka kuma, akwai wasu fitattun mutane da ke nuna goyon baya ga kawancen adawa da shugaban kasa Tinubu da APC, amma har yanzu ba su shiga ADC ba. Wannan rukuni ya hada da tsohon dan takarar shugaban kasa na Labour Party kuma tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi.



