Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta dakatar da matukan jirgin sama biyu na kamfanin ValueJet bisa zargin karya dokokin tsaro na jiragen sama a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Hukumar ta ce matukan sun fara aiwatar da shirin tashi daga wurin da aka ware musu ba tare da samun sahalewar tashi kamar yadda doka ta tanada ba. Saboda haka, NCAA ta janye lasisinsu nan take.
Daraktan Harkokin Jama’a da Kariya ga Masu Amfani da Sabis na NCAA, Mista Michael Achimugu, ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da aka fitar da yammacin ranar Talata, inda ya ce hukumar ta samu rahoton karya doka daga kansu matukan.
A cikin wani bidiyo na daƙiƙa 23 da hukumar NCAA ta wallafa a shafinta na X (wanda aka fi sani da Twitter a da), an ga jirgin CRJ-900ER mai lambar rajista 5N-BXS yana motsi daga wurin ajiya yayin da wasu ma’aikatan ƙasa ke tsaye kusa da jirgin – alamar cewa bai samu izinin tashi ba tukuna.
Wasu daga cikin ma’aikatan filin jirgin an ga su na guje-guje yayin da jirgin ke tafiya da sauri daga wurin ajiya, lamarin da hukumar NCAA ta bayyana a matsayin “harsashiyar sakaci” da ta jefa rayukan ma’aikatan kasa da sauran masu amfani da filin jirgin cikin haɗari.
Sanarwar ta ce:
“Binciken farko ya nuna cewa matukin ya fara shirin ficewa daga wurin da aka ware masa ba tare da bin dokokin tantance izinin tashi ba.
Wannan mummunan mataki ya jefa ma’aikatan kasa da sauran jama’a cikin hadari, kuma ya saba wa ƙa’idodin dokar sufuri ta jiragen sama na cikin gida da na duniya.
NCAA na kallon wannan lamari da matukar muhimmanci.”
Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa an dakatar da lasisin Captain Oluranti Ogoyi da First Officer Ivan Oloba nan take, kuma dakatarwar za ta ci gaba har zuwa lokacin da cikakken bincike zai kammala.
NCAA ta jaddada cewa tana nan daram wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin fasinjoji da ma’aikatan jiragen sama, tare da jan kunnen dukkan masu ruwa da tsaki su girmama dokoki da ka’idojin tsaro a harkar sufuri.



