Wani mutum mai shekaru 45 da haihuwa, Udeme Sunday Uko, ya rasa ransa bayan da aka harbe shi har lahira a cikin coci yayin da yake barci tare da matarsa da ’ya’yansa a garin Ikot Oku Usung da ke Jihar Akwa Ibom, da safiyar Litinin.
Matarsa, Mfon Udeme Sunday, ce ta gano lamarin da safe sannan ta sanar da shugaban matasan yankin, wanda ya garzaya ya kai rahoto ga ’yan sanda.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Akwa Ibom, DSP Timfon John, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba. Ya ce tawagar ’yan sanda ta kai ziyara wurin da lamarin ya faru inda suka gano bindiga kirar gida da harsashi daya da aka harba, wanda aka dauka a matsayin shaida.
A cewar rundunar, an gano Uko da harbin bindiga a kansa wanda ya yi sanadin mutuwarsa. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:10 na dare. Rundunar ta bayyana cewa ana bincike ko lamarin kisan gilla ne ko kuma kisan kai da ya yi wa kansa, inda ta jaddada cewa binciken yana matakin farko.
An kai gawar mamacin zuwa dakin ajiye gawa domin gudanar da binciken likita (autopsy).
Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, CP Baba Mohammed Azare, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike cikin gaggawa domin gano musabbabin mutuwar da kuma gurfanar da duk wanda aka samu da hannu cikin lamarin.
Rundunar ta tabbatar wa jama’a cewa tana amfani da dukkan hanyoyin da suka dace domin gudanar da sahihin bincike kuma za a ci gaba da sanar da jama’a da zarar sabbin bayanai sun fito.



