Aiki Mazaba: Dan Majalisar Tarayya Ya Sabunta Makabartu 80 a Zamfara

Dan Majalisar Tarayya Kabiru Ahmadu Maipalace

Wani dan majalisar wakilai daga jihar Zamfara, Kabiru Maipalace, ya dauki nauyin gyaran makabartu 80 a kananan hukumomin Gusau da Tsafe a matsayin wani bangare na ayyukan mazabarsa.

Mr. Maipalace, wanda ke wakiltar mazabar Gusau/Tsafe a Majalisar Wakilai ta Tarayya, ya bayyana haka ne yayin kaddamar da aikin a garin Tsafe ranar Talata.

A cewarsa, “Yau mun kaddamar da aikin gyaran makabartu 80 a cikin kananan hukumomin Gusau da Tsafe, a matsayin wani bangare na bikin cika shekaru biyu na zagayowar wa’adina na biyu a Majalisar Wakilai.”

“Mun lura da yadda makabartu ke cikin matsanancin hali a sassa daban-daban na mazabata. A matsayina na dan Adam, mun san cewa kowane rai zai mutu kuma zai zauna a cikin irin wannan wuri. Don haka, wajibi ne mu kyautata yanayin makabarta wacce ita ce ‘gidajenmu na ƙarshe’,” inji Maipalace.

Ya kara da cewa, “Kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, akwai falala da muhimmanci wajen gyara da kula da makabartu. Yin haka yana rage aukuwar bala’o’i da fitintinu a cikin al’umma.”

Dan majalisar ya kuma yi alkawarin biyan albashi ga masu gadi da ma’aikatan makabartu, tare da samar musu da kayan aiki a kowane wata.

Ya bukaci al’ummar mazabarsa da su kara himma wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da kawo karshen matsalolin tsaro a jihar.

Haka kuma, Maipalace ya roki jama’a da su ci gaba da goyon bayan manufofi da shirye-shiryen gwamnati domin tabbatar da zaman lafiya da cigaba a Zamfara.

A nasa jawabin, Hakimin Tsafe Gabas, Alhaji Aliyu Abubakar, ya yaba wa dan majalisar bisa wannan gagarumin aiki, yana mai cewa hakan ya dace da bukatun jama’a.

Ya kuma bukaci sauran ‘yan siyasa da su yi koyi da Maipalace wajen aiwatar da ayyukan da za su amfana wa jama’a.

“Madadin Majalisar Sarakunan Tsafe, muna mika godiya ga dan majalisar da tawagarsa saboda wannan muhimmin aiki da kuma sauran ayyukan da yake gudanarwa domin rage matsalolin zamantakewa da tattalin arziki a cikin al’umma,” inji shi.