Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya soki ‘yan siyasa da ke yakin neman zabe da alkawarin yin wa’adin mulki guda daya kacal, yana mai bayyana irin wannan alkawari a matsayin maras tushe, ruɗi, kuma alamar rashin lafiyar hankali.
Soludo, wanda ya yi magana ne a wani gangamin siyasa da aka gudanar a Anambra South ranar Asabar domin tallata aniyarsa ta tsayawa takara a wa’adi na biyu, ya ce duk wani ɗan siyasa da ke cewa zai yi zango ɗaya ya kamata a kai shi asibitin mahaukata domin duba lafiyar kwakwalwarsa.
“Ina tambaya: kana zuwa wajen mutane ka ce zango daya za ka yi? Duk wani ɗan siyasa da ke cewa hakan, ya kamata a kai shi gidan mahaukata, saboda ba shakka akwai matsala da tunaninsa,” in ji Soludo.
Wannan furuci na Soludo na zuwa ne bayan wasu kalamai da Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi kwanan nan, inda ya goyi bayan tsarin shugabancin kasa na zango daya na shekaru shida.
Haka kuma, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a 2023 kuma tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya bayyana cewa yana buɗe don shugabanci na zango daya, duba da batun adalci da tsarin rabon iko (zoning).
A wata hira da yayi a shirin Sunday Politics na Channels Television ranar 6 ga Yuli, Obi ya ce: “Zango daya ya isa wajen kafa nagartaccen shugabanci. Idan wasu na iya janyo mana matsala cikin shekaru biyu, me yasa wani ba zai iya kawo sauyi cikin shekaru hudu ba?
“Haka kuma, wannan ra’ayin yana da nasaba da mutunta yarjejeniyar rabon iko, wanda yake daya daga cikin abubuwan da ke daidaita siyasar kasar nan, ko da yake ba a rubuce take ba a cikin kundin tsarin mulki.
“Shekaru biyu ma na iya sauya komai zuwa alheri. Mutane na bukatar shugaba wanda zai tashi da safe yana nuna kulawa da jin kai ga al’umma.”
Furucin Soludo na ci gaba da janyo martani daga masu ruwa da tsaki a harkar siyasa, yayin da batun wa’adin mulki da tsarin rabon iko ke kara daukar hankalin jama’a a fagen siyasar Najeriya.



