Minista Ga Gwamna Bago: Hukumar NBC Kaɗai Ke Da Ikon Soke Lasisin Gidan Rediyo

Ministan Labarai Idris MambaMuhammad

Ministan Watsa labarai da daidaita Ra’ayi na Ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC) ce kaɗai ke da ikon dakatarwa ko soke lasisin gidan rediyo a Najeriya.

Wannan martani na minista na zuwa ne bayan umarnin da Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayar na rufe gidan rediyon Badeggi FM da ke Minna tare da kwace lasisinsa, bisa zargin yada shirye-shiryen da suka saba da ka’idojin aiki da kuma tayar da hankalin jama’a kan gwamnati.

Matakin gwamnan ya jawo mahawara da suka da martani daga kungiyoyi da dama ciki har da Amnesty International, wadda ta bayyana umarnin a matsayin harin da ke ƙoƙarin dakile ’yancin kafafen yaɗa labarai a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da mai taimakawa ministan kan harkokin yaɗa labarai, Rabiu Ibrahim, ya fitar a madadinsa a ranar Asabar, ministan ya ce yana sane da korafe-korafen da aka bayyana daga sassa daban-daban game da batun, kuma ya tabbatar da cewa gwamnati za ta tabbatar da adalci wajen warware lamarin.

“Duk da cewa muna maraba da yunkurin Gwamnatin Jihar Neja na gabatar da rahoton korafi kan Badeggi FM, yana da muhimmanci a fahimci cewa, a bisa doka, hukumar NBC ce kaɗai ke da ikon dakatar da gidan rediyo ko soke lasisinsa,” inji sanarwar.

Ministan ya ƙara da cewa, idan akwai wasu laifuka da aka yi zargin gidan rediyon ya aikata, hanya mafi dacewa ita ce a kai ƙorafi kai tsaye ga NBC domin ta gudanar da bincike da hukunci a bisa ka’ida.

“Ma’aikatar na kira ga dukkanin bangarorin da abin ya shafa da su kwantar da hankali, yayin da NBC ke da tsarin da ya dace na warware matsalar cikin gaskiya da adalci,” inji Minista Idris.

Sanarwar ta jaddada bukatar bin doka da oda da kuma mutunta kafafen yada labarai da ’yancin fadar albarkacin baki kamar yadda Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanada.