Trends

Zan iya Komawa APC, Amma da Sharudda na — Kwankwaso

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso babban jigo a jam’iyyar NNPP

Tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a zaben 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana cewa yana da shirin komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), amma ne kawai idan aka fayyace sharuddan kuma aka aiwatar da su.

A wani jawabi da ya yi a Kano, Kwankwaso ya ce:

“Idan kuka ce in shiga APC, ina so in shiga APC, ban ce ba zan shiga ba, har ma yanzu. Amma tambaya ita ce: a wace kujera? A wace manufa?”

Ya tunatar da ‘yan Najeriya rawar da shi da abokan tafiyarsa suka taka wajen kafa jam’iyyar APC, inda ya bayyana yadda suka fuskanci barazana daga EFCC, ICPC, ‘yan sanda da SSS a lokacin da suke fafutukar kafa jam’iyyar.

Sai dai ya ce ba ya gaggawar barin NNPP, domin suna cikin farin ciki a halin yanzu, amma idan akwai masu neman hadin gwiwa cikin gaskiya da adalci, ba tare da maimaita wulakanci irin na baya ba, to suna shirye.

“Ba mu cikin gaggawa mu bar NNPP; muna farin ciki. Amma idan akwai wanda zai yi aiki da mu cikin gaskiya kuma ba zai sake watsar da mu kamar a baya ba, muna nan a shirye,” in ji shi.

Sanatan ya kuma ce har jam’iyyar PDP za ta iya sake zama wani zaɓi, muddin ta amince da kura-kuranta na baya kuma ta yi alkawari a fili na gyara.

Kwankwaso ya yi korafi cewa duk da irin rawar da suka taka wajen kawo APC kan karagar mulki, gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi watsi da su tsawon shekara takwas.

“Ba a ba mu komai ba, ko godiya ma babu. Da muka koma PDP, ma a can aka hana mu kujerar shugaban yanki. Sun yi tunanin idan mun bar su, za mu bace mu mutu a daji. Amma yau duk wanda zai ambaci ‘yan siyasar Najeriya dole sai ya ambaci Kwankwaso,” in ji shi.

Maganganun Kwankwaso sun fara tayar da sabbin cece-kuce kan yiwuwar sake canjin akidu da hadin kan jam’iyyun siyasa yayin da ake kara matsowa kusa da babban zaben gaba.