Kungiyar kwallon kafa ta Skyline FC ta fito a matsayin zakaru a gasar kwallon kafa ta NFSG Football Tournament, inda ta doke Unique Football Academy da ci 3-0 a wasan karshe.
Wasan karshe ya gudana ne a filin wasan Dawaki Football Stadium, a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Mai daukar nauyin gasar, Nwovu Friday Simon Gabby, wanda shi ne Shugaba na 043 Football Club, ya bayyana cewa an shirya gasar ne domin gano sababbin ‘yan wasa da kuma shirya su don manyan dama a nan gaba.
“Zan ce na gamsu da sakamakon wannan gasa saboda mun gano ‘yan wasa masu inganci, kuma za mu ci gaba da horar da su tsawon wata guda mai zuwa,” in ji shi.
Ya kara da cewa kwallo ba wai iya buga wasa bane kawai, amma tana bukatar ladabi da kuma hakuri.
“Da jajircewa da dagewa, tabbas za mu samu kwararrun ‘yan wasa da za su iya taka leda a kungiyoyin Turai bayan gasar da za a sake gudanarwa a watan Oktoba,” in ji shi.
Shi ma kocin Skyline FC, Chile Innocent, ya danganta nasarar kungiyarsa ga aiki tukuru da himma.
“Na zo da niyyar cin nasara kuma na yi imani za mu yi nasara saboda irin aikin da muka yi kafin gasar. Ina godiya ga mai daukar nauyi da ya ba mu damar nuna basira, abokan karawa da suka ba mu kalubale, da kuma magoya baya da suka mara mana baya,” in ji shi.
A daya bangaren, Nwoma Jude, kyaftin din Unique FA, ya amince da rashin nasarar su, yana mai cewa:
“Mun shiga wasa da niyyar cin nasara, amma yau ba ranar mu bace. Za mu dauki darasi daga wannan gasa, mu shirya don wadda za ta biyo baya.”
Shugaban Kwamitin Shirya Gasar, Shuaibu Idris, ya yaba wa mai daukar nauyin gasa bisa goyon bayan matasa, inda ya bukaci gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki su tallafa irin wadannan shirye-shirye.

“Shirye-shiryen gasar ba su zo ba tare da kalubale ba, amma ina alfahari yadda aka kammala ta cikin nasara,” in ji shi.
Haka zalika, wani bako na musamman a gasar, Ishaya Yakubu, ya yi jawabi na kwarin gwiwa ga ‘yan wasa:
“Ina taya zakaru murna, amma ya kamata mu sani a kwallo duka kungiyoyi zakaru ne, saboda jajircewa, kokari, da jarumtar da aka nuna. Kowa ya yi iya kokarinsa don cin nasara; babu wanda ya fito da niyyar faduwa. Amma a kwallo wani lokaci rana ba ta yi maka ba, dole a koyi zama da hakuri. Muna fatan ganin ku a tawagar kasa nan gaba. Ina taya Skyline FC murna.”
Skyline FC ta karbi kofin gasar tare da kyautar kudi na Naira 500,000, yayin da Unique FA ta samu Naira 300,000 a matsayin ta biyu.
Rahoton First TV ya nuna cewa gasar NFSG Football Tournament ta kunshi kungiyoyi 13 daga fadin Babban Birnin Tarayya, inda aka fafata daga ranar 10 ga Agusta zuwa 31 ga Agusta, 2025.
