Trends

Tsohon Ministan Sufurin Sirika, Ya Nesanta Kansa da Kungiyar Hadin Kan ADC

Hadi Sirika Tsohon Ministan sufurin Jirgin Sama

Hadi Sirika, tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, a ranar Laraba ya karyata rahotannin da ke alakanta shi da wata kungiyar adawa da ake cewa tana shirin hambarar da Shugaba Bola Tinubu a shekarar 2027.

Tsohon Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a shirin Morning Brief na gidan talabijin na Channels TV, inda ya ce ba shi da wani hannu a cikin wannan kungiya kuma ba zai taba shiga cikinta ba.

An ruwaito cewa Sirika ya halarci bikin kaddamar da African Democratic Congress (ADC), jam’iyyar da aka zaba a matsayin abin hawa na siyasa domin kalubalantar jam’iyyar APC a zaben 2027.

Da aka tambaye shi kan rahotannin da ke alakanta shi da wannan hadin gwiwa, Sirika ya ce kai tsaye: “A’a, ba ni ba ne.”

Ya kara da cewa:
“Jiya ina tare da Cif Bayo Onanuga a Fadar Shugaban Kasa, sai ya ce ina cikin kungiyar hadin kai. Na shaida masa cewa ba ni bane kuma ba zan taba shiga ba. Ya ce ya samu labarin daga rahotanni. Mutane na iya shiga kungiyoyi, hakan shi ne dimokuradiyya.”

Haka kuma, da aka tambaye shi kan ziyarar da ya kai kwanan nan Aso Rock, tsohon Ministan ya bayyana cewa manufar ziyarar shi ne kawai ya je ya mika sakon ta’aziyya ga Shugaba Tinubu, bayan rasuwar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

A cewarsa:
“Dalilin ganawarmu shi ne don mu mika ta’aziyya ga Shugaban Kasa, wanda ya nuna bajinta sosai bayan rasuwar jagoranmu, Shugaba Muhammadu Buhari.”