Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya, Nigeria Labour Congress (NLC), ta yi barazanar kaddamar da yajin aikin gama-gari a faɗin ƙasa kan abin da ta kira “karɓar kuɗi ta tilas da aka kafawa tsari” a ɓangaren wutar lantarki, tana mai zargin ci gaba da rugujewar grid da kuma rashin ƙaruwa a samar da wuta fiye da shekaru goma bayan sayar da kamfanonin gwamnati ga masu zaman kansu.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana haka a Abuja yayin taron ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Ƙasa (National Union of Electricity Employees), inda ya bayar da “gargaɗi na ƙarshe” ga hukumomi da masu gudanar da kamfanonin wuta, yana mai cewa za su yi tsayin daka kan duk wani ƙarin kuɗin wuta ko manufofin da ke ƙara wa jama’a wahala ba tare da inganta wadatar wuta ba.
Ajaero ya nuna damuwa cewa yawan samar da wuta har yanzu na tsakanin megawatt 4,000 zuwa 5,000 kacal — kusan yadda yake tun bayan raba tsohuwar Power Holding Company of Nigeria (PHCN) — duk da ƙaruwar buƙata.
A cewarsa, “Maimakon ci gaba, muna ganin koma baya. Maimakon haske, muna cikin duhu.”
NLC ta kuma soki rarraba masu amfani da wuta zuwa rukunan Band A, B da C, tana mai cewa wata hanya ce ta ɓoye don ƙara kuɗin wuta.
“Banding wata kafa ce ta karɓar kuɗi ta tilas. Masu amfani da Band A na biyan kuɗi mai tsada amma har yanzu suna samun wuta mai yankewa-yankewa. Ana tilasta wa ‘yan Najeriya biyan kuɗin duhu,” in ji Ajaero.
Ƙungiyar ta kuma soki shirin gwamnatin tarayya na bayar da tallafin Naira tiriliyan 3 ga kamfanonin samar da wuta (GenCos), tana mai kiran sa “tallafi na bogi” da yunƙurin ɓoye don amfanar da masu zuba jari da suka gaza kafin zaɓen 2027.
“Duk wata kobo a baitul-mali mallakin ma’aikata da al’ummar Najeriya ne,” in ji shi.
NLC ta buƙaci a sake duba batun sayar da kamfanonin wuta ga masu zaman kansu, tana mai jaddada cewa dole ne a ɗauki wutar lantarki a matsayin hidimar jin ƙai ta jama’a.
A cewar Ajaero, “Misalan duniya sun nuna babu ƙasar da ta samu nasarar tafiyar da ɓangaren wuta gaba ɗaya bisa neman riba kaɗai ba tare da jefa jama’a cikin wahala ba.”
Ƙungiyar ta buƙaci a kira Babban Taron Masu Ruwa da Tsaki na Ƙasa domin tsara wata “Taswirar Wutar Jama’a” da za ta ba fifiko ga wuta mai araha, tabbatacciya, farashi mai dacewa da sabis, da kuma jarin gwamnati a ɓangaren samarwa da rarraba wuta.
Duk da cewa gwamnati na aiwatar da wasu gyare-gyare ciki har da shirin dala biliyan 2.5 don biyan basussuka da inganta kayayyakin more rayuwa, NLC ta ce a shirye take ta tattara ma’aikata da al’umma domin tsayawa kan duk wani abu da ta kira cin zarafi, tana mai cewa:
“Al’ummar Najeriya ba za su ci gaba da biyan kuɗin duhu ba. Dole ne a mayar da wuta hannun jama’a.”






