Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa har yanzu ba a tabbatar da tsaron wasu kananan hukumomi hudu na jihar Borno ba, don gudanar da aikin ci gaba da rajistar masu kada kuri’a (CVR) na shekarar 2025/2026 a hedikwatocinsu.
Kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da Abadam, Guzamala, Kala-Balge da Marte.
Kwamishinan Zabe na Jihar Borno, Abubakar Ahmed Ma’aji, ne ya bayyana haka a taron manema labarai da aka gudanar a Maiduguri ranar Juma’a.
“Don dalilan tsaro da kiyaye rayuka, ofisoshin INEC na kananan hukumomi hudu za su gudanar da rijistar kai-tsaye a wuraren da ke cikin birnin Maiduguri.”
Ma’aji ya bayyana wuraren da aka tanada kamar haka:
Masu halartar rajista daga Abadam za su yi rajista a Yerwa Peace, Baga Road, Maiduguri.
Masu halartar daga Guzamala za su yi rajista a Fire Service Department, 1,000 Housing Estate, Maiduguri.
Masu halartar daga Kala-Balge za su yi rajista a Goni Kachallari Primary School, Mafa Road, Maiduguri.
Masu halartar daga Marte za su yi rajista a Kachamari, opposite Shettiram Filling Station, Gamboru-Ngala Road, Maiduguri.
Ya ce aikin zai gudana a matakai uku:
Mataki na 1: 28 ga Agusta – 10 ga Disamba 2025, tare da nuna jerin sunaye daga 15 – 21 ga Disamba 2025.
Mataki na 2: 5 ga Janairu – 17 ga Afrilu 2026, tare da nuna jerin sunaye daga 20 – 26 ga Afrilu 2026.
Mataki na 3: 4 ga Mayu – 17 ga Agusta 2026, tare da nuna jerin sunaye daga 24 – 30 ga Agusta 2026.
Ma’aji ya ce wannan aiki kira ne na kasa ga kowane dan kasa mai cancanta don yin rawar gani a tsarin dimokuradiyya, inda ya yi alkawarin cewa INEC za ta samar da bayanai akai-akai har zuwa kammala aikin.
Ya kuma roki hadin kan kafafen yada labarai da jama’a don ganin an cimma nasara.



