Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana cewa tana da cikakken kwarin gwiwar lashe dukkan kujerun shugabannin kananan hukumomi 23 a jihar Rivers a zaben da za a gudanar ranar 30 ga Agusta, 2025.
Mataimakin Shugaban APC na Kasa, Kudu maso Kudu, Cif Victor Giadom, ya bayyana haka a taron kaddamar da yakin neman zaben kananan hukumomi na APC da aka gudanar a Captain Elechi Amadi Polytechnic, Rumuola, a karamar hukumar Obio/Akpor ranar Alhamis.
Yayin da ya ke wakiltar Giadom, Sanata Magnus Abe ya jinjinawa cewa APC a matsayin babbar jam’iyyar adawa a jihar, ta kara karfi da hadin kai gabanin zaben. Ya yaba da jagorancin Cif Tony Okocha wajen hada kan mambobi, abin da ya ce ya zama abin kishi ga jam’iyyun adawa.
Ya kuma yaba wa shugabannin jam’iyyar a jihar bisa gudanar da zaben fidda gwani cikin lumana da ya fitar da ‘yan takara nagari. Ya ce:
“APC a jihar Rivers ta hade. APC a jihar Rivers tana da karfi. APC a jihar Rivers tana shirye ta kawo wa talakawa romon dimokiradiyya. Kowa a jihar Rivers ana maraba da shi a APC. Mu hada kai. Ku ne fuskar Renewed Hope Agenda a matakin kananan hukumomi. Mu na da yakinin ba za ku ba mu kunya ba.”
Shi ma shugaban APC na jihar, Cif Tony Okocha, wanda ya mika tutar jam’iyya ga ‘yan takara na shugabancin kananan hukumomi 23 da mataimakansu, ya soki zaben da aka gudanar a zamanin tsohon Gwamna Siminalayi Fubara a matsayin “wasa-wasa” wanda ya sa APC ta kaurace masa.
“Mun ce ba za mu shiga ba, muka kuma nuna musu cewa ba zai yiwu ba, kuma bai yiwu ba. Yau muna farin ciki da cewa tsarin da hukumar RSIEC ta tanada ya dace, shi ya sa muka fito tare da goyon baya. A zaben 30 ga Agusta ba wai gwaji za mu yi ba, za mu shiga gasar kuma mu ci gaba da nasara a kananan hukumomi 23 da mazabu 319 na jihar Rivers.”
Okocha ya kuma gode wa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, bisa hada kan ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban domin marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaben 2027.
Ya umurci ‘yan takara da su gudanar da yakin neman zabe cikin lumana, yana mai cewa:
“Ku je ku yi yakin neman zabe. Jam’iyyarmu ba ta son tashin hankali. Mun fito da jam’iyya daga halin durkushewa, yanzu muna kan gaba, mu ci gaba da kiyaye wannan matsayi da inganci.”



