Amurka da Iran sun amince da tsagaita wuta na makonni biyu bisa sharadi, wanda zai ba jiragen kasuwanci damar wucewa cikin mashigar ruwan Strait of Hormuz, lamarin da ya rage tashin hankalin da aka shafe makonni ana fama da shi bayan hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra’ila kan wasu wurare a Iran.
Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, ne ya sanar da yarjejeniyar da sanyin safiyar ranar Laraba, bayan ya shiga tsakani wajen sasanta bangarorin biyu. Tsagaita wutar ya fara aiki nan take.
Yarjejeniyar ta zo ne sa’o’i kadan bayan shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi gargadin cewa za a dauki mataki mai tsauri idan Iran ba ta bude mashigar ruwan ba. Daga baya ya bayyana cewa ya amince da “dakatar da hare-hare kan Iran na tsawon makonni biyu,” bisa sharadin cewa Tehran za ta bari zirga-zirgar jiragen ruwa ta ci gaba ba tare da tangarda ba.
Iran ta tabbatar da cewa za ta ba jiragen ruwa damar wucewa cikin mashigar, karkashin kulawar sojojinta, tare da gabatar da shirin abubuwa guda 10.
Shirin ya hada da bukatar dakatar da rikice-rikice a Iran, Iraq, Lebanon da Yemen, dage takunkumi, sakin kudaden da aka toshe, da kuma biyan diyya don sake gina wuraren da aka lalata. Haka kuma ta sake jaddada kudirinta na kin mallakar makaman nukiliya.
Duk da tsagaita wutar, har yanzu ana cikin fargaba. An ji karar kararrawa a Isra’ila jim kadan bayan sanarwar, inda rundunar sojin Isra’ila ta ce ta dakile wasu makamai masu linzami.
Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa na goyon bayan dakatar da hare-haren Amurka na wucin gadi, amma ya jaddada cewa tsagaita wutar “ba ya shafar Lebanon,” inda har yanzu ake ci gaba da farmakin kasa kan kungiyar Hezbollah.
Pakistan ta gayyaci wakilai daga kasashen biyu zuwa Islamabad ranar Juma’a domin ci gaba da tattaunawa. Fadar White House ta tabbatar da cewa ana tattaunawa, amma ta ce har yanzu ba a kammala shirya wani taro ba.
Masu harkokin diflomasiyya sun gargadi cewa tattaunawar za ta kasance mai wahala, ganin yadda Amurka da Iran ke da sabanin fahimta kan sharuddan tsagaita wutar. Yunkurin tattaunawa da aka yi a baya cikin shekarar da ta gabata ya gamu da cikas sakamakon sabbin hare-haren soja.
