Trends

Martanin Nafi’u Bala ga Kwankwaso “Kai Ɗan Leƙen Asiri Ne a ADC”

Nafiu Bala Gombe, wani jagoran ɓangare na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya mayar da martani ga tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, kan rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar.

Jam’iyyar ADC, wadda ke zama mafakar wasu jagororin adawa da ke shirin kalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027, ta fada cikin rikicin shugabanci a ‘yan kwanakin nan.

Rikicin cikin gida na ci gaba da tsananta yayin da bangaren Bala da kuma bangaren da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, ke jagoranta ke ikirarin su ne halastattun shugabannin jam’iyyar.

Kwankwaso, wanda ya shiga ADC kwanan nan gabanin zaben 2027, ya bayyana damuwa cewa Bala ya ki amsa gayyatar da aka masa domin sasanta rikicin.

A wata hira da DCL Hausa, Kwankwaso ya ce Bala mai shekaru 35 ne, yana mai cewa jagoran bangaren ya rasa shawarar uba.

Sai dai da yake mayar da martani, Bala ya karyata batun shekarunsa tare da zargin tsohon gwamnan Kano da zama kamar ɗan leƙen asiri na jam’iyyar APC.

Bala ya gargadi Kwankwaso cewa ba shi da hurumin tsoma baki cikin rikicin shugabancin jam’iyyar, yana mai cewa ya kamata manyan ‘yan siyasa su ajiye burinsu su bai wa matasa damar jagorantar harkokin jam’iyya.

Ya ce shi ba mai shekaru 35 ba ne kamar yadda Kwankwaso ya fada, yana mai bayyana cewa yana da shekaru 46.
“Ko da ni matashi ne, Kwankwaso ba shi da ikon raina ni,” in ji Bala Gombe, yana mai tuna wa Kwankwaso cewa shi da wasu daga cikin shugabannin siyasar yau sun rike manyan mukamai tun suna matasa.

Bala ya kara da cewa ya kamata Kwankwaso da sauran manyan ‘yan siyasa su ba matasa dama kamar yadda aka ba su a lokacin da suke tasowa, su koma taka rawar ba da shawara kawai.

“Su bar matasa su jagoranci jam’iyyunmu da kuma kasar nan, su kuma su tsaya a matsayin masu ba da shawara,” in ji shi.

Ya kuma tuna cewa a shekarar 2023, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tare da wasu manyan Arewa sun nemi Kwankwaso ya janye takararsa domin hadin kan kuri’un Arewa, amma ya ki amincewa.

“Da ya ki janyewa a wancan lokacin, ba shi da wata hujja ta yin min barazana ko ba ni shawara kan rashin adalcin da ake yi min a ADC. Ba wanda zai iya tsorata ni,” in ji Bala Gombe.