Trends

Taron ADC: PDP Karƙashin Jagorancin Wike ta Nesanta Kanta da Ɓangaren Turaki

Nyesom Wike Ministan Babban Birnin Tarayya

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta karyata rahotannin da ke cewa ta yi wani zama da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), inda ta bayyana zarge-zargen a matsayin marasa tushe kuma masu yaudara.

A cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa, Jungudo Haruna Mohammed, ya fitar a ranar Laraba, jam’iyyar ta ce ba ta kira ko amince da wani zama da ADC ko wakilanta ba.

PDP ta ƙara da cewa duk wasu mutane da ake zargin sun shiga irin waɗannan tattaunawa sun yi hakan ne a matsayinsu na kashin kansu, kuma ba su wakiltar jam’iyyar ba.

Sanarwar ta ce: “PDP na bayyana karara cewa ba ta yi wani zama ba, na hukuma ko na ba hukuma ba, da ADC ko wani daga cikin wakilanta,” tare da kira ga mambobinta, magoya bayanta da kuma al’umma da su yi watsi da irin waɗannan rahotanni.

Jam’iyyar ta kuma jaddada cewa ta maida hankali kan shirye-shiryen zabubbukan fidda gwani da ke tafe, inda ta ce shirye-shiryen sun kai wani mataki mai zurfi. Ta ƙara da cewa za ta sanar da jadawali da ƙa’idojin gudanar da zabukan nan gaba kaɗan.

A ƙarshe, PDP ta tabbatar da kudurinta na bin tsare-tsaren cikin gida tare da burinta na samar da shugabanci nagari ga ‘yan Najeriya.