Hukumar Kididdiga ta Ƙasa, National Bureau of Statistics (NBS), ta bayyana cewa Najeriya ta samu ƙaruwa mai yawa a shigo da jari a rubu’i na uku na shekarar 2025, inda jimillar shigo da jari ta kai dala biliyan 6.01.
Wannan adadi ya nuna ƙaruwa da kashi 380 cikin ɗari idan aka kwatanta da dala biliyan 1.25 da aka samu a rubu’i na uku na 2024, sannan ya karu da kashi 17.5 cikin ɗari daga dala biliyan 5.12 a rubu’i na biyu na 2025, lamarin da ke nuna ci gaba da sha’awar masu zuba jari a tattalin arzikin ƙasar.
Bincike ya nuna cewa zuba jari a hannun jari (portfolio investment) ne ya mamaye shigo da jarin, inda ya kai dala biliyan 4.85 (80.7%), sannan sauran nau’ikan zuba jari (other investments) suka kai dala miliyan 864.6 (14.4%). Zuba jari kai tsaye daga ƙasashen waje (Foreign Direct Investment – FDI) shine ƙaramin kaso, inda ya kai dala miliyan 296.3 (4.9%).
Bisa fannin masana’antu, bangaren banki ya jawo dala biliyan 3.14 (52.3%), yayin da bangaren kudi da hada-hadar kuɗi ya samu dala biliyan 1.86 (30.9%). Masana’antu da samar da kayayyaki sun karɓi dala miliyan 261.4 (4.4%).
A ƙasashen da suka fi bayar da jari, Ƙasar United Kingdom ta fi kowacce, inda ta bayar da dala biliyan 2.94 (48.8%), sai Amurka da dala miliyan 950.5 (15.8%), sannan Afirka Ta Kudu da dala miliyan 774 (12.9%). Wadannan ƙasashe uku sun samar da mafi yawan shigo da jari.
Daga cikin manyan cibiyoyin kudi, Standard Chartered Bank Nigeria Limited ta samu dala biliyan 2.12 (35.2%), Stanbic IBTC Bank Plc ta jawo dala biliyan 1.79 (29.8%), yayin da Citibank Nigeria Limited ta samu dala miliyan 561.4 (9.3%).
Masana tattalin arziki sun ce rinjayar zuba jari ta hannun jari na nuna cewa masu zuba jari na ƙasashen waje na da amincewa da tsarin kuɗi na Najeriya, duk da cewa ƙarancin FDI na nuna akwai ƙalubale a tsarin jari da zuba jari na dogon lokaci.
Rahoton NBS ya tabbatar cewa shigo da jari ya kai kololuwa cikin shekaru shida na dala biliyan 16.7 a cikin watanni tara na farko na 2025, wanda ke nuna ƙaruwar jawo hankalin masu zuba jari na duniya ga Najeriya.







