Ƙungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta shigar da ƙara a kan Central Bank of Nigeria (CBN) kan zargin bacewa ko karkatar da kuɗaɗen jama’a har Naira tiriliyan 3.
An shigar da ƙarar ne a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, inda SERAP ke kuma neman a yi bayani kan Naira biliyan 629 da aka ce an biya wa “wadanda ba a san su ba” ƙarƙashin shirin Anchor Borrowers’ Programme.
A cikin wata sanarwa, SERAP ta ce ta ɗauki matakin ne bayan “munanan zarge-zarge” da ke kunshe cikin rahoton shekara-shekara na 2025 na Babban Mai Binciken Kuɗaɗen Tarayya (Auditor-General of the Federation), wanda aka wallafa a ranar 9 ga Satumba.
Ƙungiyar ta ce, “Wadannan zarge-zarge masu muni daga Mai Binciken Kuɗaɗen Tarayya na nuna yiwuwar take amana mai tsanani, saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima), dokar CBN, da kuma ƙa’idojin yaƙi da cin hanci da rashawa.”
SERAP ta yi zargin cewa yiwuwar karkatar da kuɗin na nuna gazawar tsarin ɗaukar alhaki a babban bankin ƙasar, lamarin da ke raunana amincewar jama’a kan yadda ake tafiyar da dukiyar ƙasa.
Ta jaddada cewa ‘yan Najeriya na da haƙƙin sanin yadda ake sarrafa kuɗaɗen jama’a. “’Yan Najeriya na da haƙƙin sanin inda kuɗaɗen da aka ce sun bace ko aka karkatar suke,” in ji ƙungiyar, tana mai cewa bayyana gaskiya na da muhimmanci wajen dawo da amincewa ga cibiyoyin gwamnati.
Ƙarar, mai lamba FHC/ABJ/CS/250/2026, na neman kotu ta bayar da umarnin mandamus da zai tilasta wa CBN bayyana inda kuɗaɗen suke da kuma cikakken bayanin yadda aka kashe su.
SERAP ta ƙara da cewa amincewa da bukatun da ta gabatar a kotu zai taimaka wajen dawo da dukiyar da ta dace da kuma hana sake faruwar irin waɗannan zarge-zarge a nan gaba.







