Rundunar Sanda ta Gayyaci El-Rufai da Shugabannin Jam’iyyar ADC a Kaduna

Dan sanda

Rundunar Yan Sanda ta Jihar Kaduna ta gayyaci tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai, domin ya bayyana a gaban ta kan zargin hada baki da aikata laifi, tunzura jama’a, tayar da tarzoma, da kuma jikkata mutane.

Wannan kiran ya fito ne daga Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda mai kula da binciken manyan laifuka, Zubairu Abdullahi, wanda ya hada da wasu manyan shugabannin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) na jihar.

A cikin takardar gayyatar, rundunar ta bayyana cewa El-Rufai da sauran shugabannin ADC, ciki har da Shugaban Yammacin Arewa maso Yammacin jam’iyyar, Ja’afaru Sani, an gayyace su domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen hada baki, tayar da hankalin jama’a, da kuma barna.

Takardar ta ce: “Wannan sashen bincike yana gudanar da bincike kan karar da aka shigar game da wasu mambobin jam’iyyarku. Ana bukatarku ku zo tare da wadanda aka ambata zuwa SCID domin fayyace zarge-zargen da masu korafi suka gabatar a ranar 8 ga Satumba, 2025.”

Sun hada da: Malam Nasir El-Rufai, Bashir Saidu, Ja’afaru Sani, Ubaidullah Mohammed (wanda aka fi sani da Mikiya 30), Nasiru Maikano, Aminu Abita, da Ahmed Rufa’i Hussaini (wanda aka fi sani da Mikiya).

Sai dai a nasa bangaren, mambobin jam’iyyar ADC sun bayyana cewa ba su samu takardar gayyatar daga ‘yan sanda ba, illa kawai sun karanta labarin a shafukan sada zumunta.