Trends

Philip Aduda Ya Fice Daga PDP Zuwa APC

Tsohon Sanatan da ya wakilci Babban Birnin Tarayya (FCT), Philip Aduda, ya sanar a ranar Talata cewa ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) tare da komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Aduda ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne sakamakon rikicin cikin gida da ke addabar PDP.
Bayan ya fice daga jam’iyyar, nan take ya ziyarci hedikwatar APC, inda shugaban jam’iyyar na kasa, Nentawe Yilwatda, ya tarbe shi.

A cikin wasikar murabus dinsa, Aduda ya nuna godiyarsa ga PDP bisa damar da jam’iyyar ta ba shi na rike mukamai daban-daban na zabe a tsawon lokaci.

Aduda, wanda ya yi aiki a Majalisar Dattawa ta 9, ya sha kaye a zaben 2023 a hannun Ireti Kingibe. Tun daga lokacin, yana aiki kafada da kafada da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, a wani matsayi na ba a hukumance ba.

A lokuta da dama, Wike ya soki yadda Kingibe ke gudanar da aikinta, yana mai cewa ba za ta sake komawa Majalisar Dattawa ba.