Sabon Ministan Kuɗi kuma Ministan Tattalin Arziki na Ƙasa, Taiwo Oyedele, ya karɓi ragamar aiki a hukumance, inda ya yi alƙawarin ci gaba da ƙarfafa gyare-gyaren tattalin arziki da kuma samar da fa’ida ga ‘yan ƙasa ta hanyar manufofi masu ƙarfafa ci gaba da bin ƙa’idojin kashe kuɗi yadda ya kamata.
Oyedele ya karɓi mukamin ne daga wanda ya gada, Wale Edun, wanda ya yaba masa bisa kafa tubali mai ƙarfi na farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.
A cikin jawabin karɓar aiki, sabon ministan ya bayyana cewa Najeriya na cikin wani muhimmin mataki na tattalin arziki, inda ya ce dole ne a gina kan matakan da aka ɗauka na daidaita al’amura ta hanyar zurfafa gyare-gyaren da za su inganta rayuwar jama’a da dawo da amincewa da tattalin arzikin ƙasa.
Ya bayyana manyan manufofi guda biyar da zai mayar da hankali a kai, ciki har da ƙara yawan samar da kayayyaki da bunƙasa tattalin arziki ta hanyar samar da yanayin kasuwanci mai kyau ga masu zuba jari, wanda ke dogara da daidaito, tsari da bayyana manufofi a sarari.
Oyedele ya kuma yi alƙawarin ƙarfafa kula da kuɗaɗen gwamnati ta hanyar amfani da su cikin hikima da gaskiya domin tabbatar da dorewar tattalin arziki.
Dangane da tara kuɗaɗen shiga, ya ce gwamnati za ta aiwatar da tsarin haraji mai adalci ta hanyar haɗa hanyoyin karɓar haraji, faɗaɗa tushen haraji, rage nauyi a kan marasa ƙarfi, tare da tallafa wa bunƙasar tattalin arziki.
Haka kuma, ya yi alƙawarin ƙarfafa haɗin kai tsakanin dukkan matakan gwamnati da cibiyoyi domin tabbatar da cewa manufofi na haifar da sakamako mai inganci.
Ministan ya kuma bayyana haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu a matsayin ginshiƙi na manufofinsa, yana mai cewa zurfafa hulɗa da ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki zai taimaka wajen tsara manufofi bisa sahihan bayanai da kuma tabbatar da aiwatar da su yadda ya kamata.
A cewarsa, kyawawan manufofi kaɗai ba za su wadatar ba, domin nasara na buƙatar aiwatarwa mai inganci, ɗaukar alhaki da kuma sakamako mai auna.
Oyedele ya ce yana fatan yin aiki tare da jami’an gwamnati, ɓangaren masu zaman kansu da kuma ‘yan Najeriya domin ɗaukar ƙasa daga “gyara zuwa sakamako,” da saurin bunƙasa tattalin arziki, tare da gina ƙasa mai ɗorewa, mai haɗin kai da wadata.
