Obi Ya Fice Daga jam’iyyar Labour Zuwa ADC

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, Peter Obi, ya sanar da sauya sheka zuwa African Democratic Congress (ADC).

Obi, tsohon gwamnan Jihar Anambra, ya bayyana hakan ne yayin jawabin sabuwar shekara da ya gabatar a Nike Lake Resort da ke Enugu. Ya ce matakin da ya dauka ya samo asali ne daga kishin kasa da kuma bukatar gina babbar hadakar kasa domin fuskantar kalubalen tattalin arziki, zamantakewa da dimokuradiyya da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

A cewarsa, Najeriya ta kai wani mataki mai hadari da ba za a ci gaba da siyasar rarrabuwar kawuna ba. Ya yi kira ga ’yan Najeriya, shugabannin adawa da kuma mambobin Obidient Movement da su hada kai karkashin jam’iyyar ADC a matsayin dandalin hadin gwiwa domin “ceto Najeriya daga talauci, rashin hadin kai da tabarbarewar dimokuradiyya.”

“Wannan shawara na daukar ta ne bisa kishin kasa da muradin kasa kawai. Ina rokon abokan siyasa na da shugabannin adawa a fadin kasar nan da su shiga wannan babbar hadakar kasa karkashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC). Tarihi ba zai yafewa shiru a irin wannan lokaci mai hatsari ga kasa ba,” in ji Obi.

Yayin da yake bayyana sauya shekar a matsayin wani bangare na babban aiki na kasa, Obi ya ce Najeriya na kammala shekarar 2025 a wani muhimmin mataki da ke bukatar tsayayyen buri da jagoranci mai karfi. Ya ce halin da kasar ke ciki a yau ba saboda karancin albarkatu ba ne, illa gazawar shugabanci.

“Najeriya ba talakawa ba ce; an sace ta aka jefa ta cikin talauci. Kasa ba ta karye ba; an ci amanarta. Mutanenmu masu aiki tukuru ne kuma masu basira, amma tsarin mulki yana bai wa rashin kwarewa lada tare da sake jujjuya gazawa,” in ji shi.

Obi ya bayyana mummunan halin da kasar ke ciki ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa, inda ya ambaci yawaitar talauci, rashin aikin yi da matsalar tsaro. Ya ce sama da ’yan Najeriya miliyan 130 na rayuwa cikin talauci mai yawa, yayin da fiye da matasa miliyan 80 ke fama da rashin aikin yi, yana mai cewa wannan hali bai dace da girman Najeriya da yawan al’ummarta ba.

Ya kuma zargi ’yan siyasa masu mulki da amfani da bambancin kabila da addini domin ci gaba da rike iko, yana mai cewa irin wannan dabaru sun lalata hadin kan kasa da ci gaban da ya shafi kowa.

Dangane da sahihancin zabe, Obi ya gargadi cewa sauye-sauyen zabe ba abin tattaunawa ba ne, yana mai jaddada cewa dole ne a kare amincin zaben 2027. Ya yi gargadin duk wani yunkuri na magudin zabe, yana mai cewa sahihin zabe shi ne ginshikin tsirar dimokuradiyyar Najeriya.

Yana kwatanta Najeriya da wasu kasashe da ya ziyarta a duniya, Obi ya ce kasashen da suka fara da irin matsayin da Najeriya ta fara sun samu gagarumin ci gaba ta hanyar shugabanci mai tsari da hadin kan kasa. Ya ambaci Indonesia a matsayin misali, yana mai cewa duk da cewa kasashen biyu sun taba kasancewa a matsayi daya, Indonesia ta zama tattalin arziki mai darajar tiriliyan daloli, yayin da Najeriya ke fama da durkushewar masana’antu, cin hanci da rashawa da karuwar talauci.

Obi ya kuma soki sauye-sauyen haraji na Gwamnatin Tarayya, yana mai kiran su da marasa amfani ga jama’a kuma masu cutar tattalin arziki. Ya ce zargin da ake yi na dokar haraji ta bogi, idan har gaskiya ne, zai iya gurgunta amincewar jama’a da kuma hadin kan kasa.

Yana kallon sauya shekar sa zuwa ADC a matsayin shiri na zaben 2027, Obi ya ce hadin kan ’yan adawa shi ne kadai hanyar da za ta iya kayar da abin da ya kira gwamnati da ke rayuwa kan rarrabuwar kawuna da farfaganda. Ya kara da cewa aikin da ke gaba na bukatar sadaukarwa, jarumtaka da hadin gwiwa.